Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tar 34:19-33 Littafi Mai Tsarki (HAU)

19. Da sarki ya ji irin maganganun da littafin ya faɗa, sai ya yayyage tufafinsa.

20. Sa'an nan sarki ya umarci Hilkiya, da Ahikan ɗan Shafan, da Akbor ɗan Mika, da magatakarda Shafan, da Asaya baran sarki, ya ce,

21. “Ku tafi ku yi tambaya a wurin Ubangiji domina, da kuma domin sauran waɗanda suka ragu a Isra'ila da Yahuza, a kan abin da littafin da aka gāno ya faɗa, gama Ubangiji ya yi fushi da mu da hasala mai tsanani saboda kakanninmu ba su kiyaye maganar Ubangiji, su aikata bisa ga dukan abin da aka faɗa a wannan littafi ba.”

22. Hilkiya kuwa tare da waɗanda sarki ya aika suka tafi wurin annabiya Hulda, matar Shallum ɗan Tikwa, ɗan Harhas, mai lura da wurin ajiyar tufafi, tana zaune a Urushalima, a unguwa ta biyu. Suka faɗa mata saƙon sarki,

23. sai ta ce musu, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra'ila, ya ce in faɗa wa mutumin da ya aiko gare shi,

24. ‘Ni Ubangiji, na ce zan kawo masifa a kan wannan wuri da a kan mazaunan wurin, wato dukan la'anar da aka rubuta a littafin da aka karanta a gaban Sarkin Yahuza.

25. Da yake sun bar bina suka ƙona turare ga gumaka domin su sa ni in yi fushi da dukan ayyukan hannuwansu, saboda haka zan yi fushi da wannan wuri, ba kuwa zan huce ba.’

26. Amma a kan Sarkin Yahuza wanda ya aike ku ku tambayi Ubangiji, ga abin da za ku faɗa masa, ‘Ni Ubangiji, Allah na Isra'ila na ce, a kan maganar da ka ji,

27. da yake zuciyarka mai tuba ce, ka kuma ƙasƙantar da kanka a gaban Allah, sa'ad da ka ji maganarsa a kan wurin nan da mazaunan wurin, ka kuma ƙasƙantar da kanka a gabana, ka yayyage tufafinka ka yi kuka a gabana, ni kuma na ji ka.

28. Ga shi, zan kai ka wurin da kakanninka suke, a kabarinka a binne ka da salama, ba za ka ga dukan masifun da zan kawo wa wurin nan da mazaunansa ba.’ ”Sai suka isar da amsa wurin sarki.

29. Sarki ya aika a kirawo dukan dattawan Yahuza da na Urushalima.

30. Sai sarki ya haura zuwa Haikalin Ubangiji tare da dukan mutanen Yahuza, da mazaunan Urushalima, da firistoci, da Lawiyawa, da dukan jama'a, babba da yaro. Sai ya karanta dukan maganar da take a littafin alkawari wanda aka gāno a Haikalin Ubangiji, a kunnen dukansu.

31. Sai sarkin ya miƙe tsaye a inda yake, ya yi alkawari a gaban Ubangiji, cewa zai bi Ubangiji, ya kiyaye umarnansa, da farillansa, da dokokinsa da zuciya ɗaya, da dukan ransa. Zai yi aiki da alkawarin da yake rubuce a wannan littafi.

32. Ya kuma sa dukan waɗanda suke a Urushalima da na Biliyaminu, su tsaya a kan wannan magana. Mazaunan Urushalima kuwa suka yi yadda alkawarin Allah ya ce, wato Allah na kakanninsu.

33. Yosiya kuwa ya kawar da dukan abubuwan banƙyama daga dukan ƙasar da jama'ar Isra'ila suke da ita. Ya sa dukan waɗanda suke a Isra'ila su bauta wa Ubangiji Allahnsu. A dukan kwanakin ransa, ba su kauce daga bin Ubangiji Allah na kakanninsu ba.

Karanta cikakken babi 2 Tar 34