Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tar 26:11-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Har yanzu kuma, Azariya yana da rundunar sojoji waɗanda suka iya yaƙi ƙungiya ƙungiya, yadda Yehiyel magatakarda, da Ma'aseya jarumi, suka karkasa su bisa ga umarnin Hananiya, ɗaya daga cikin 'yan majalisar sarki.

12. Jimillar shugabannin gidajen kakanni na ƙarfafan mutane jarumawa, dubu biyu da ɗari shida (2,600) ne.

13. Suna da sojoji dubu ɗari uku da dubu bakwai da ɗari biyar (307,500) a ƙarƙashin ikonsu waɗanda suke da ƙarfin yin yaƙi sosai, da za su taimaki sarki a kan maƙiyansa.

14. Azariya ya shirya wa sojojinsa garkuwoyi, da māsu, da kwalkwali, da sulke, da bakuna, da duwatsun majajjawa.

15. A Urushalima ya yi na'urori waɗanda gwanayen mutane ne suka ƙago don a sa su a hasumiya, da kan kusurwoyi, don a harba kibau, da manyan duwatsu. Da haka sunansa ya bazu ko'ina, gama ya sami taimako mai banmamaki, har ya zama mai ƙarfin gaske.

16. Amma sa'ad da ya yi ƙarfi, sai ya shiga girmankai, wanda ya zamar masa hallaka. Sai ya yi izgili a gaban Ubangiji Allahnsa, ya shiga Haikalin Ubangiji don ya ƙona turare a bisa bagaden ƙona turare.

17. Amma Azariya firist, ya bi shi tare da firistoci tamanin na Ubangiji, mutane ne jarumawa.

18. Sai suka hana sarki Azariya, suka ce masa, “Ba aikinka ba ne, Azariya, ka ƙona turare ga Ubangiji, wannan aikin firistoci ne, 'ya'yan Haruna, waɗanda aka keɓe su don ƙona turare. Fita daga wurin nan mai tsarki, gama ka yi kuskure, ba za ka sami daraja daga wurin Ubangiji Allah ba.”

19. Azariya ya yi fushi, a lokacin kuwa yana riƙe da farantin ƙona turare a hannunsa, sa'ad da ya yi fushi da firistocin, sai kuturta ta faso a goshinsa, a nan gaban firistocin a cikin Haikalin Ubangiji, wajen bagaden ƙona turare.

20. Sai Azariya babban firist tare da sauran firistocin suka dube shi, sai ga kuturta a goshinsa! Sai suka tunkuɗa shi waje nan da nan. Shi kansa ma ya hazarta ya fita saboda Ubangiji ya buge shi.

21. Ta haka sarki Azariya ya kuturce, har zuwa ranar mutuwarsa. Saboda kuturtarsa, ya zauna a keɓe a wani gida, gama an fisshe shi daga Haikalin Ubangiji. Yotam ɗansa shi ya shugabanci iyalin gidan sarki, yana kuma mulkin jama'ar ƙasa.

22. Sauran ayyukan Azariya, daga farko har zuwa ƙarshe, annabi Ishaya ɗan Amoz ya rubuta su.

23. Azariya ya rasu, suka binne shi tare da kakanninsa a hurumin sarakuna, gama suka ce, “Shi kuturu ne.” Sai Yotam ɗansa ya gāji gadon sarautarsa.

Karanta cikakken babi 2 Tar 26