Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tar 13:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A shekara ta goma sha takwas ta mulkin sarki Yerobowam, sai Abaija ya ci sarautar Yahuza.

2. Ya yi mulki shekara uku a Urushalima, sunan tsohuwarsa Ma'aka, 'yar Uriyel na Gibeya.Sai yaƙi ya ɓarke a tsakanin Abaija da Yerobowam.

3. Abaija ya tafi da rundunar jarumawansa, dubu ɗari huɗu (400,000) zaɓaɓɓun mutane. Yerobowam shi kuma ya jā dāgar yaƙi don ya kara da Abaija, yana da mutum dubu ɗari takwas (800,000), zaɓaɓɓun mayaƙa ƙarfafa.

4. Sai Abaija ya hau kan Dutsen Zemarayim, wanda yake a ƙasar Ifraimu mai tuddai, ya ce, “Ku kasa kunne gare ni, ya Yerobowam da dukanku Isra'ilawa.

5. Ashe, ba ku sani ba, Ubangiji Allah na Isra'ila, ya ba da sarautar Isra'ila ga Dawuda, da 'ya'yansa maza har abada, ta wurin alkawarin gishiri?

6. Duk da haka Yerobowam ɗan Nebat, baran Sulemanu ɗan Dawuda, ya tashi, ya yi wa ɗan ubangidansa tawaye,

7. waɗansu marasa amfani, 'yan iska, suka taru suka goyi bayansa, suka raina Rehobowam ɗan Sulemanu, saboda a lokacin shi yaro ne, ba shi da ƙarfin zuciya, bai iya tsayayya da su ba.

8. Yanzu kuma, so kuke ku ƙi mulkin Ubangiji wanda yake hannun 'ya'yan Dawuda, maza, saboda yawan da kuke da shi, da gumakan maruƙan zinariya da kuke da su, waɗanda Yerobowam ya yi muku.

9. Ashe, ba ku kori firistocin Ubangiji, 'ya'yan Haruna, maza, da Lawiyawa ba, kuka yi wa kanku firistoci kamar na al'umman sauran ƙasashe? Duk wanda ya zo ya miƙa ɗan bijimi da raguna bakwai don ya tsarkake kansa, ya zama firist na gumaka ke nan, ba na Allah ba.

10. “Amma a gare mu, Ubangiji shi ne Allahnmu, ba mu kuwa rabu da shi ba. Muna da firistoci, 'ya'yan Haruna, maza, masu yi wa Ubangiji hidima, da Lawiyawa masu yi musu hidima.

11. Safe da yamma suna miƙa wa Ubangiji hadayun ƙonawa, da turare mai daɗin ƙanshi, sukan ajiye gurasar ajiyewa a kan tebur ɗin zinariya tsantsa, sukan lura da alkukin zinariya, da kuma fitilunsa kowane maraice, gama muna riƙe da umarnin Ubangiji Allahnmu, amma ku kun rabu da shi.

Karanta cikakken babi 2 Tar 13