Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sar 7:6-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. gama Ubangiji ya sa sojojin Suriyawa suka ji amon karusai, da na dawakai, da na babbar rundunar soja. Sai suka ce wa junansu, “Ai, Sarkin Isra'ila, ya yi ijara da sarakunan Hittiyawa, da na Masarawa, su zo su fāɗa mana.”

7. Saboda haka suka gudu da almuru, suka bar alfarwansu, da dawakansu, da jakunansu, suka bar sansanin yadda yake, suka tsira da rayukansu.

8. Sa'ad da kutaren nan suka zo sansanin, sai suka shiga wata alfarwa, suka ci suka sha. Suka kwashe azurfa, da zinariya, da tufafi, suka tafi suka ɓoye. Suka koma suka shiga wata alfarwa kuma, suka kwashe abubuwan da suke cikinta. Suka tafi suka ɓoye su.

9. Sa'an nan suka ce wa junansu, “Ba mu kyauta ba. Yau ranar albishir ce, idan mun yi shiru, mun jira har safe, wani mugun abu zai same mu. Domin haka bari mu tafi mu faɗa a gidan sarki.”

10. Sai suka tafi wurin masu gadin ƙofar birnin, suka ce musu, “Mun tafi sansanin Suriyawa ba mu ga kowa ba, ba mu kuma ji motsin kowa a wurin ba, ba kowa a wurin sai dawakai da jakai, a ɗaure, alfarwai kuma suna nan yadda suke.”

11. Sa'an nan masu tsaron ƙofar birnin suka aika a faɗa a gidan sarki.

12. Sai sarki ya tashi da dare ya ce wa fādawansa, “Bari in faɗa muku irin shirin da Suriyawa suka yi a kanmu. Sun sani muna fama da yunwa, domin haka suka fita daga sansanin suka ɓuya a karkara, suna nufin sa'ad da muka fita daga birnin, sai su kama mu da rai, sa'an nan su shiga birnin.”

13. Ɗaya daga cikin fādawan sarki ya ce, “A sa waɗansu mutane su ɗauki dawakai biyar da suka ragu cikin birnin, idan ba su tsira ba, za su zama kamar sauran Isra'ilawan da suka riga suka mutu. Bari mu aika, mu gani.”

14. Aka ɗibi mahayan dawakai biyu, sarki kuwa ya aike su, su bi bayan sojojin Suriyawa, ya ce musu, “Ku tafi, ku gani.”

15. Sai suka bi bayansu har zuwa Kogin Urdun, suka ga tufafi da makamai barjat ko'ina a hanya, waɗanda Suriyawa suka zubar lokacin da suke gudu. Sai manzannin suka komo suka faɗa wa sarki.

Karanta cikakken babi 2 Sar 7