Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sar 15:8-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. A shekara ta talatin da takwas ta sarautar Azariya Sarkin Yahuza, Zakariya ɗan Yerobowam na biyu, ya ci sarautar Isra'ila a Samariya wata shida.

9. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji kamar yadda kakanninsa suka yi. Bai rabu da zunuban Yerobowam ɗan Nebat ba, wanda ya sa mutanen Isra'ila su yi zunubi.

10. Shallum ɗan Yabesh ya ƙulla masa maƙarƙashiya, ya buge shi a Ibleyam, ya kashe shi, sa'an nan ya hau gadon sarautarsa.

11. Sauran ayyukan da Zakariya ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila.

12. Wannan shi ne alkawarin da Ubangiji ya yi wa Yehu, cewa 'ya'yansa maza za su zauna a gadon sarautar Isra'ila har tsara ta huɗu. Haka kuwa ya zama.

13. Shallum ɗan Yabesh ya ci sarauta a shekara ta talatin da tara ta sarautar Azariya Sarkin Yahuza. Ya yi mulki wata ɗaya a Samariya.

14. Menahem ɗan Gadi daga Tirza ya zo Samariya ya bugi Shallum ɗan Yabesh a Samariya, ya kashe shi, ya hau gadon sarautarsa.

15. Sauran ayyukan Shallum duk da makircin da ya ƙulla, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila.

16. A lokacin nan sai Menahem ya hallaka Tifsa da dukan waɗanda suke cikinta, da karkararta tun daga Tirza, domin ba su karɓe shi ba, saboda haka ya hallaka ta, ya tsattsage dukan matan da suke da juna biyu.

17. A shekara ta talatin da tara ta sarautar Azariya, Sarkin Yahuza, Menahem ɗan Gadi, ya ci sarautar. Ya yi shekara goma a Samariya.

18. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji. A dukan kwanakinsa bai rabu da zunubin Yerobowam ɗan Nebat ba, wanda ya sa mutanen Isra'ila su yi zunubi.

19. Tiglatfilesar, mai mulkin Assuriya, ya kawo wa ƙasar yaƙi, Menahem kuwa ya ba Tiglat-filesar talanti dubu (1,000) na azurfa, don dai ya taimake shi yadda sarautarsa za ta kahu sosai.

20. Menahem ya karɓi kuɗin daga mutanen Isra'ila, wato daga attajirai. Ya tilasta wa kowannensu ya ba da azurfa hamsin. Saboda haka Tiglat-filesar mai mulkin Assuriya ya koma ƙasarsa.

21. Sauran ayyukan Menahem, da dukan abin da ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila.

22. Menahem ya mutu, ɗansa Fekahiya ya gaji sarautarsa.

Karanta cikakken babi 2 Sar 15