Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sam 5:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Dukan kabilan Isra'ila kuwa suka zo wurin Dawuda a Hebron, suka ce, “Ga shi, mu 'yan'uwanka ne.

2. A dā sa'ad da Saul yake sarautarmu, kai kake bi da Isra'ilawa zuwa yaƙi, kai kake komo da su. Ubangiji kuma ya ce maka, ‘Kai za ka lura da jama'ata Isra'ila, za ka zama sarkinsu.’ ”

3. Sai dukan dattawan Isra'ila suka tafi wurin sarki Dawuda a Hebron, shi kuwa ya yi alkawari da su a gaban Ubangiji. Su kuwa suka naɗa shi Sarkin Isra'ila duka.

4. Dawuda ya ci sarauta yana da shekara talatin. Ya yi shekara arba'in yana sarauta.

5. Ya yi sarautar jama'ar Yahuza shekara bakwai da wata shida a Hebron. Ya kuma yi sarautar jama'ar Isra'ila duk da Yahuza shekara talatin da uku a Urushalima.

6. Sarki Dawuda da mutanensa suka tafi Urushalima su yaƙi Yebusiyawa mazaunan ƙasar. Su kuwa suka ce wa Dawuda, “Ba za ka iya zuwa nan ba, makafi kawai da guragu za su kore ka.” A zatonsu Dawuda ba zai iya zuwa can ba.

7. Duk da haka Dawuda ya ci kagarar Sihiyona, wato birnin Dawuda.

8. A ran nan Dawuda ya ce, “Duk wanda zai kashe Yebusiyawa, to, sai kuma ya haura zuwa wuriyar ruwa ya fāɗa wa guragu da makafi waɗanda ran Dawuda yake ƙi.” Don haka a kan ce, “Makafi da guragu ba za su shiga Haikali ba.”

9. Dawuda ya zauna a kagara. Ya ba ta suna Birnin Dawuda. Ya kuma yi gine-gine kewaye da wurin. Ya fara daga Millo zuwa ciki.

10. Dawuda kuwa ya ƙasaita, gama Ubangiji Allah Mai Runduna yana tare da shi.

11. Hiram Sarkin Taya ya aiki jakadu zuwa wurin Dawuda. Ya kuma aika masa da katakan itacen al'ul, da kafintoci, da masu yin gini da duwatsu, suka kuwa gina wa Dawuda gida.

Karanta cikakken babi 2 Sam 5