Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sam 18:15-32 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Sa'an nan samari goma masu ɗaukar wa Yowab makamai, suka kewaye Absalom, suka yi ta dūkansa har ya mutu.

16. Sa'an nan Yowab ya busa ƙaho, sojoji suka komo daga runtumar Isra'ilawa. Yowab ya tsai da su.

17. Suka ɗauki gawar Absalom, suka jefa ta cikin wani rami mai zurfi a kurmin, suka tula tsibin duwatsu a kanta. Dukan Isra'ilawa kowa ya tsere zuwa gidansa.

18. Tun Absalom yana da rai ya gina wa kansa al'amudi a kwarin sarki, gama ya ce, “Ba ni da ɗa wanda zai sa a riƙa tunawa da ni.” Ya kira al'amudin da sunansa. Ana kuwa kiransa al'amudin Absalom har wa yau.

19. Ahimawaz ɗan Zadok ya ce wa Yowab, “Ka yarda mini in sheƙa a guje in kai wa sarki labari yadda Ubangiji ya cece shi daga hannun magabtansa.”

20. Yowab ya ce masa, “Ba za ka kai labari yau ba, sai wata rana ka kai, amma yau ba za ka kai labari ba, domin ɗan sarki ya mutu.”

21. Sa'an nan Yowab ya ce wa wani mutumin Habasha, “Tafi ka faɗa wa sarki abin da ka gani.” Sai Bahabashen ya rusuna wa Yowab, sa'an nan ya sheƙa a guje.

22. Ahimawaz ɗan Zadok kuma ya ce wa Yowab, “Ko mene ne zai faru dai, ka bar ni in bi bayan Bahabashen a guje.”Yowab ya ce masa, “Don me za ka tafi, ɗana, tun da yake ba za ka sami lada saboda labarin da za ka kai ba?”

23. Ahimawaz ya ce, “Duk dai abin da zai faru, zan tafi.”Sai Yowab ya yardar masa ya tafi. Sa'an nan Ahimawaz ya sheƙa, ya bi ta hanyar fili, ya wuce Bahabashen.

24. Dawuda kuwa yana zaune a tsakanin ƙofofi biyu na garin. Mai tsaro ya hau kan soron da yake kan bangon garu. Da ya ɗaga kai ya duba, sai ya ga mutum yana gudu shi kaɗai.

25. Ya ta da murya, ya faɗa wa sarki. Sai sarki ya ce, “Idan shi kaɗai ne, yana kawo labari ne.” Mutumin ya yi ta ƙara zuwa kusa.

26. Mai tsaron kuma ya ga wani mutum yana zuwa shi ma a guje, sai ya ta da murya wajen mai ƙofar garin, ya ce, “Ga wani mutum kuma yana zuwa a guje!”Sai sarki ya ce, “Shi ma labari yake kawowa.”

27. Mai tsaron ya ce, “Na ga gudun na farin kamar gudun Ahimawaz ɗan Zadok.”Sai sarki ya ce, “Shi mutumin kirki ne, yana kawo kyakkyawan labari ne.”

28. Da Ahimawaz ya zo kusa da sarki, ya ce, “Salama!” Sa'an nan ya rusuna a gaban sarki ya sunkuyar da fuska ƙasa, ya ce, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allahnka, wanda ya ba da mutanen da suka tayar wa ubangijina, sarki.”

29. Sai sarki ya ce, “Na ce dai, saurayin nan, Absalom, yana nan lafiya?”Ahimawaz ya amsa, ya ce, “A sa'ad da Yowab ya aiko ni na ga babban hargitsi, amma ban san ko mene ne ba.”

30. Sarki kuwa ya ce, “Koma waje ɗaya, ka tsaya.” Sai ya koma waje ɗaya ya tsaya cik.

31. Sai ga Bahabashe ya iso, ya ce, “Abishirinka, ya ubangijina, sarki, gama a wannan rana ta yau Ubangiji ya cece ka daga hannun waɗanda suka tayar maka.”

32. Sarki ya tambaye shi, “Na ce dai, saurayin nan Absalom, yana lafiya?”Bahabashen ya amsa, “Allah ya sa abokan gāban ubangijina, sarki, da duk waɗanda suka tayar maka da mugunta, su zama kamar saurayin nan.”

Karanta cikakken babi 2 Sam 18