Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sar 2:32-45 Littafi Mai Tsarki (HAU)

32. Ubangiji zai ɗora masa alhakin mugayen ayyukansa, gama ya kashe mutum biyu ba da sanin tsohona Dawuda ba, waɗanda kuma suka fi shi adalci, wato Abner ɗan Ner, shugaban sojojin Isra'ila, da Amasa ɗan Yeter, shugaban sojojin Yahuza.

33. Don haka alhakin jininsu zai koma a kan zuriyar Yowab har abada, amma da Dawuda da zuriyarsa, da gidansa, da gadon sarautarsa, albarkar Ubangiji za ta zauna a kansu har abada.”

34. Benaiya ɗan Yehoyada kuwa ya shiga alfarwar ya kashe shi. Aka binne shi a gidansa a karkara.

35. Sa'an nan sarki ya naɗa Benaiya ɗan Yehoyada, shugaban sojoji a maimakon Yowab, ya kuma naɗa Zadok, firist, a maimakon Abiyata.

36. Sai kuma sarki ya aika a kirawo Shimai. Sa'an nan ya ce masa, “Ka gina wa kanka gida a Urushalima, ka zauna a nan, kada ka fita ko kaɗan zuwa wani wuri.

37. Gama ran da ka fita, ka haye rafin Kidron, ka tabbata fa za ka mutu, alhakin jininka kuwa zai koma kanka.”

38. Shimai kuwa ya ce wa sarki, “Abin da ka faɗa daidai ne, abin da ka ce in yi, zan yi, ranka ya daɗe.” Sai Shimai ya zauna a Urushalima kwanaki da yawa.

39. Amma bayan shekara uku, sai biyu daga cikin bayin Shimai suka gudu zuwa wurin Akish ɗan Ma'aka, Sarkin Gat. Da aka faɗa wa Shimai, cewa bayinsa suna a Gat,

40. sai ya tashi, ya yi wa jakinsa shimfiɗa, ya tafi Gat wurin Akish don neman bayinsa. Ya kuwa komo da bayinsa daga Gat.

41. Da aka faɗa wa Sulemanu, cewa Shimai ya fita Urushalima, ya tafi Gat, ya komo

42. sai ya aika a kirawo Shimai, ya ce masa, “Ashe, ban sa ka ka rantse da Ubangiji ba, na kuma dokace ka da ƙarfi, cewa ka tabbata ran da ka fita zuwa ko'ina za ka mutu? Kai kuma ka ce mini, ‘Abin da ka ce daidai ne, zan yi biyayya.’

43. To, me ya sa ka karya rantsuwar da ka yi da sunan Ubangiji, da kuma umarnin da na umarce ka?”

44. Sarki kuma ya ce masa, “Ka sani sarai irin duk muguntar da ka yi wa tsohona, Dawuda. Haka kuma Ubangiji zai sāka maka bisa ga muguntarka.

45. Amma Ubangiji zai sa mini albarka, ya kuma tabbatar da gadon sarautar Dawuda har abada.”

Karanta cikakken babi 1 Sar 2