Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 18:6-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Sa'ad da sojoji suke komowa gida, bayan da Dawuda ya komo daga kisan Goliyat, sai mata daga kowane gari na Isra'ila suka fito domin su taryi sarki Saul. Suna raira waƙar farin ciki, suna rawa, suna kaɗa kuwaru da molaye.

7. Suka raira waƙa, suna cewa, “Saul ya kashe dubbai, amma Dawuda ya kashe dubun dubbai.”

8. Wannan waƙa ta ba Saul haushi, ya ce, “Sun ba Dawuda dubun dubbai, amma dubbai kawai suka ba ni, me kuma ya rage masa, ai, sai sarauta.”

9. Tun daga wannan rana Saul ya fara kishin Dawuda.

10. Kashegari Allah ya sa mugun ruhu ya sauka a kan Saul, sai ya yi ta maganganu a gidansa kamar mahaukaci, sai Dawuda ya yi ta kaɗa masa garaya kamar yadda ya saba yi. Saul kuwa yana riƙe da mashi.

11. Yana cewa a ransa, “Zan nashe shi in kafe shi da bango.” Sau biyu yana cakar Dawuda da mashi, amma Dawuda ya goce.

12. Saul ya ji tsoron Dawuda, gama Ubangiji yana tare da Dawuda, amma ya rabu da Saul.

13. Saboda haka Saul bai yarda Dawuda ya zauna tare da shi ba, amma ya maishe shi shugaban dubu. Shi kuwa ya riƙa bi da su cikin kai da kawowa.

14. Dawuda kuwa ya yi ta yin nasara cikin ayyukansa duka, domin Ubangiji yana tare da shi.

15. Da Saul ya ga Dawuda yana yin nasara, sai ya ƙara jin tsoronsa.

16. Dukan mutanen Isra'ila da na Yahuza suka ƙaunaci Dawuda, domin yana kai da kawowa a cikinsu.

17. Sai Saul ya ce wa Dawuda, “Ga Merab babbar 'yata, zan ba ka ita ka aura, idan ka yi mini aikin jaruntaka, wato ka yi yaƙin Ubangiji.” (Gama Saul yana tsammani ta wannan hanya Filistiyawa za su kashe Dawuda, ba lalle sai shi da kansa ya kashe shi ba.)

18. Dawuda, ya ce wa Saul, “Wane ni ko iyalin mahaifina a cikin Isra'ila, har da zan zama surukin sarki?”

19. Amma sa'ad da lokaci ya yi da za a ba Dawuda Merab, 'yar Saul, ya aura, sai aka aurar da ita ga Adriyel, mutumin Abel-mehola.

Karanta cikakken babi 1 Sam 18