Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 17:23-39 Littafi Mai Tsarki (HAU)

23. Sa'ad da yake magana da su, sai ga Goliyat, jarumin Filistiyawa na Gat, ya fito daga rundunar Filistiyawa, ya yi maganganu irin na dā. Dawuda kuwa ya ji.

24. Sa'ad da dukan mazajen Isra'ila suka ga mutumin, suka guje masa saboda tsoro.

25. Suka ce, “Kun ga mutumin nan da ya fito? Lalle ya fito ne don ya nuna mana raini. Duk wanda ya kashe shi, sarki zai arzutar da shi, ya ba shi 'yarsa aure, ya kuma 'yantar da gidan mahaifinsa cikin Isra'ila.”

26. Sai Dawuda ya tambayi mutanen da suke kusa da shi, ya ce, “Me za a yi wa wanda ya kashe Bafilisten nan, har ya kawar da zargi daga Isra'ila? Gama wane ne wannan Bafiliste, marar kaciya, da zai raina rundunar Allah mai rai?”

27. Mutane suka maimaita masa abin da sarki ya faɗa.

28. Lokacin da Dawuda yake magana da mutanen, sai Eliyab babban wansa ya ji, ya husata, ya ce wa Dawuda, “Me ya kawo ka nan? Wa ka bar wa 'yan tumakin nan a jeji? Na san rigimarka da taurinkanka, ka zo ne don ka yi kallon yaƙi.”

29. Dawuda kuwa ya ce, “To, me kuma na yi, ba tambaya kawai na yi ba?”

30. Sai ya rabu da shi ya tafi wurin wani, ya sāke yin tambaya irin ta dā, mutane kuma suka ba shi amsa irin ta dā.

31. Sa'ad da waɗansu suka ji maganar da Dawuda ya yi, sai suka faɗa wa Saul. Shi kuwa ya aika a kira Dawuda.

32. Dawuda kuwa ya ce wa Saul, “Kada zuciyar kowa ta karai saboda wannan mutum, baranka zai tafi ya yi yaƙi da shi.”

33. Saul ya ce wa Dawuda, “Ba za ka iya yaƙi da wannan Bafiliste ba, gama kai ɗan saurayi ne, shi kuwa ya saba da yaƙi tun yana saurayi.”

34. Amma Dawuda ya ce wa Saul, “Ai, baranka makiyayin tumakin mahaifinsa ne, sa'ad da zaki ko beyar ya zo ya kama ɗan rago daga garken,

35. nakan bi shi in fāɗa masa, in ƙwato ɗan ragon daga bakinsa. Idan ya tasar mini da faɗa, sai in kama reronsa, in buge shi, in kashe shi.

36. Baranka ya taɓa kashe zaki da beyar, wannan arne zai zama kamar ɗaya daga cikinsu, tun da yake ya raina rundunar Allah mai rai.

37. Ubangiji wanda ya cece ni daga dāgin zaki da na beyar, zai cece ni daga hannun wannan Bafiliste.”Sa'an nan Saul ya ce wa Dawuda, “Tafi, Ubangiji ya taimake ka.”

38. Ya sa wa Dawuda kayan yaƙinsa, ya sa masa kwalkwalin tagulla a kansa, ya kuma sa masa sulke.

39. Da Dawuda ya sa kayan yaƙin, ya rataya takobi, ya fara tafiya, sai ya ji ba zai iya ba, domin bai saba da su ba. Sai ya ce wa Saul, “Ba zan iya tafiya da waɗannan ba, gama ban saba da su ba.” Ya kuwa tuɓe su.

Karanta cikakken babi 1 Sam 17