Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

W. Yah 1:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Wahayin Yesu Almasihu da Allah ya ba shi ya nuna wa bayinsa abin da lalle ne zai auku ba da daɗewa ba, ya kuwa bayyana shi ta wurin aiko da mala'ikansa zuwa gun bawansa Yahaya,

2. wanda ya shaidi Maganar Allah, da kuma shaidar Yesu Almasihu, har da dukan abin da ya gani.

3. Albarka tā tabbata ga mai karanta maganar nan ta annabci, ta kuma tabbata ga masu ji, waɗanda kuma suke kiyaye abin da yake a rubuce a ciki, domin lokaci ya gabato.

4. Daga Yahaya zuwa ga ikilisiyoyin nan bakwai da suke a ƙasar Asiya.Alheri da salama su tabbata a gare ku daga wanda yake a yanzu, shi ne a dā, shi ne kuma a nan gaba, da kuma Ruhohin nan bakwai da suke a gaban kursiyinsa,

5. da kuma Yesu Almasihu Amintaccen Mashaidi, na farko a cikin masu tashi daga matattu, mai mulkin sarakunan duniya.Ɗaukaka da mulki su tabbata har abada abadin ga wanda yake ƙaunarmu, ya kuma ɓalle mana ƙangin zunubanmu ta wurin jininsa,

6. ya mai da mu firistoci, mallakar Allah Ubansa. Amin.

7. Ga shi, zai zo a cikin gajimare, kowa zai gan shi, har da waɗanda suka soke shi, duk kabilan duniya kuma za su yi kuka a kansa. Wannan haka yake. Amin.

8. “Ni ne Alfa. Ni ne Omega,” in ji Ubangiji Allah, wanda yake a yanzu, shi ne a dā, shi ne kuma a nan gaba, Maɗaukaki.

Karanta cikakken babi W. Yah 1