Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mar 9:19-26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

19. Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Ya ku mutanen zamani marar bangaskiya! Har yaushe zan iya zama da ku? Har yaushe kuma zan iya jure muku? Ku dai kawo mini shi.”

20. Suka kawo masa yaron. Da aljanin ya gan shi, nan da nan sai ya buge yaron, jikinsa na rawa, ya fāɗi yana ta birgima, bakinsa na kumfa.

21. Yesu ya tambayi uban yaron, “Tun yaushe wannan abu ya same shi?” Uban ya ce, “Tun yana ƙarami.

22. Ya kuwa sha jefa shi a wuta da ruwa, don ya hallaka shi. Amma in za ka iya yin wani abu, ka ji tausayinmu ka taimake mu.”

23. Sai Yesu ya ce masa, “In zan iya? Ai, dukkan abu mai yiwuwa ne ga mai ba da gaskiya.”

24. Nan da nan sai uban yaron ya ɗaga murya ya ce, “Na ba da gaskiya. A kore mini rashin bangaskiyata!”

25. Da Yesu ya ga taro na ɗungumowa a guje, sai ya tsawata wa baƙin aljanin ya ce masa, “Kai, beben aljan, na umarce ka ka rabu da shi, kada kuma ka ƙara hawansa.”

26. Bayan aljanin nan ya yi ihu, sai ya buge shi da gaske, jikinsa na rawa, ya rabu da shi. Yaron kuma ya zama kamar matacce, har ma yawancin mutane suka ce, “Ai, ya mutu!”

Karanta cikakken babi Mar 9