Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 16:8-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Suka kuwa ratsa ƙasar Misiya, suka gangara zuwa Taruwasa.

9. Wata rana da daddare aka yi wa Bulus wahayi, ya ga wani mutumin ƙasar Makidoniya na tsaye, yana roƙonsa yana cewa, “Ka ƙetaro Makidoniya, ka taimake mu mana.”

10. Da kuwa ya ga wahayin, nan take sai muka nemi tafiya Makidoniya, muka tabbata cewa Allah ne ya kira mu mu yi musu bishara.

11. Shi ke nan fa, sai muka tashi a jirgin ruwa daga Taruwasa, muka miƙe sosai har zuwa tsibirin Samutaraki, kashegari kuma sai Niyabolis,

12. daga nan kuma sai Filibi ta ƙasar Makidoniya, wadda take babbar alkarya ce a wannan waje, birnin Romawa ne kuma. A nan birnin muka yi 'yan kwanaki.

13. Ran Asabar muka fita ƙofar gari, muka je bakin kogi, inda muke tsammani akwai wurin yin addu'a. Nan muka zauna, muka yi wa matan da suka taru magana.

14. Ɗaya daga cikin masu sauraronmu wata mace ce, mai suna Lidiya, mai sayar da jar hajja, mutuniyar Tayatira, mai ibada ce kuma. Ubangiji ya buɗe zuciyarta, har ta mai da hankali ga abin da Bulus ya faɗa.

15. Da aka yi mata baftisma tare da jama'ar gidanta, ta roƙe mu ta ce, “Da yake kun amince ni mai ba da gaskiya ga Ubangiji ce, to, sai ku zo gidana ku sauka.” Sai ta rinjaye mu.

16. Wata rana muna tafiya wurin yin addu'a, sai muka gamu da wata yarinya mai aljani mai duba, tana kuwa samo wa iyayengijinta amfani mai yawa ta wurin dubar.

17. Sai ta riƙa binmu, mu da Bulus, tana ihu tana cewa, “Mutanen nan fa bayin Allah Maɗaukaki ne, suna kuwa sanar da ku hanyar ceto!”

18. Haka ta dinga yi kwana da kwanaki, har Bulus ya ji haushi ƙwarai, ya juya ya ce wa aljanin, “Na umarce ka da sunan Yesu Almasihu, ka rabu da ita.” Nan take kuwa ya rabu da ita.

Karanta cikakken babi A.m. 16