Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Rut 4:5-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Sa'an nan Bo'aza ya ce, “A ranar da ka sayi gonar daga hannun Na'omi, sai kuma ka ɗauki Rut, mutuniyar Mowab, matar marigayin, domin ka ta da zuriyar da za ta gaji marigayin.”

6. Sai dangin nan mafi kusa ya ce, “Ba zan iya ɗaukar Rut ba, domin kada in ɓata nawa gādo. Na bar maka ka ɗauke ta gama ni ba zan iya ba.”

7. Wannan ita ce al'adar Isra'ilawa a dā a kan sha'anin fansa ko musaya, don tabbatar da al'amarin. Sai mai sayarwar ya tuɓe takalminsa ya ba mai sayen. Wannan ita ce hanyar tabbatarwa a cikin Isra'ila.

8. Saboda haka a sa'ad da dangin nan mafi kusa ya ce wa Bo'aza, “Sai ka saye ta,” sai ya tuɓe takalminsa ya ba Bo'aza.

9. Sa'an nan Bo'aza ya ce wa dattawan da dukan jama'ar da suke wurin, “Yau ku ne shaidu, cewa, na sayi dukan abin da yake na Elimelek, da na Kiliyon, da na Malon daga hannun Na'omi.

10. Game da wannan kuma Rut, mutuniyar Mowab, matar marigayi Malon, ta zama matata domin in wanzar da sunan marigayin cikin gādonsa, don kada sunansa ya mutu daga na 'yan'uwansa, da kuma a garinsu. Ku ne fa shaidu a yau.”

Karanta cikakken babi Rut 4