Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Rut 4:3-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Sa'an nan ya ce wa dangin nan nasa na kusa, “Ga Na'omi wadda ta komo daga ƙasar Mowab, tana so ta sayar da gonar Elimelek danginmu.

4. Don haka na ga ya kamata in sanar da kai cewa, ka saye ta a gaban waɗanda suke zaune a nan, da a gaban dattawan jama'a. Idan za ka fanshi gonar sai ka fanshe ta, idan kuwa ba za ka fansa ba, ka faɗa mini don in sani, gama daga kai sai ni muke da izinin fansar gonar.”Sai mutumin ya ce, “Zan fanshe ta.”

5. Sa'an nan Bo'aza ya ce, “A ranar da ka sayi gonar daga hannun Na'omi, sai kuma ka ɗauki Rut, mutuniyar Mowab, matar marigayin, domin ka ta da zuriyar da za ta gaji marigayin.”

6. Sai dangin nan mafi kusa ya ce, “Ba zan iya ɗaukar Rut ba, domin kada in ɓata nawa gādo. Na bar maka ka ɗauke ta gama ni ba zan iya ba.”

7. Wannan ita ce al'adar Isra'ilawa a dā a kan sha'anin fansa ko musaya, don tabbatar da al'amarin. Sai mai sayarwar ya tuɓe takalminsa ya ba mai sayen. Wannan ita ce hanyar tabbatarwa a cikin Isra'ila.

8. Saboda haka a sa'ad da dangin nan mafi kusa ya ce wa Bo'aza, “Sai ka saye ta,” sai ya tuɓe takalminsa ya ba Bo'aza.

Karanta cikakken babi Rut 4