Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Neh 8:11-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Lawiyawa kuma suka bi suna rarrashin jama'a, suna cewa, “Ku yi shiru, gama wannan rana tsattsarka ce, kada ku yi baƙin ciki.”

12. Sai jama'a duka suka koma gidajensu suka ci, suka sha, suka aika wa wanda ba shi da abinci. Suka yi murna ƙwarai domin sun fahimta dokokin da aka karanta musu.

13. Kashegari kuma sai shugabannin kakannin gidajen jama'a duka, tare da firistoci, da Lawiyawa, suka je wurin Ezra, magatakarda, domin su yi nazarin dokokin.

14. Sai suka iske an rubuta a cikin dokokin da Ubangiji ya umarta ta hannun Musa, cewa sai jama'ar Isra'ila su zauna a bukkoki a lokacin idi na watan bakwai.

15. Saboda haka sai suka yi shela a garuruwansu duka da a Urushalima cewa, “Ku fita zuwa tuddai ku kawo rassan zaitun, da na kadanya, da na dargaza, da na dabino, da sauran rassan itatuwa masu gazari, domin a yi bukkoki kamar yadda aka rubuta.”

16. Sai suka tafi suka kawo rassan, suka yi wa kansu bukkoki a kan rufin sorayensu, da a dandalinsu, da cikin harabar Haikalin Allah, da a dandalin Ƙofar Ruwa, da a dandalin Ƙofar Ifraimu.

17. Dukan taron jama'ar da suka komo daga zaman talala suka yi wa kansu bakkoki, suka zauna cikinsu, gama tun daga kwanakin Joshuwa ɗan Nun, har zuwa wannan rana, jama'ar Isra'ila ba su yin haka. Aka kuwa yi farin ciki mai yawa.

18. Kowace rana, tun daga rana ta fari zuwa rana ta ƙarshe, Ezra yakan karanta musu daga cikin littafin dokokin Allah. Suka kiyaye idin har kwana bakwai. A rana ta takwas kuma suka muhimmin taro bisa ga ka'ida.

Karanta cikakken babi Neh 8