Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Neh 2:7-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Sa'an nan na ce wa sarki, “Idan sarki ya yarda, sai a ba ni takarda zuwa ga masu mulki da suke a lardin Yammacin Kogin Yufiretis domin su yardar mini in wuce zuwa Yahuza.

8. A kuma ba ni takarda zuwa ga Asaf, sarkin daji, domin ya ba ni katakan da zan yi jigajigan ƙofofin kagarar Haikali, da na garun birnin, da na gidan da zan zauna.” Sarki kuwa ya ba ni abin da na roƙa, gama Allah yana tare da ni.

9. Da na zo wurin masu mulkin Yammacin Kogin Yufiretis, sai na miƙa musu takardar sarki. Sarki ya haɗa ni da sarkin yaƙi da mahayan dawakai.

10. Amma Sanballat Bahorone, da Tobiya, Ba'ammone, bawa, ba su ji daɗi ba ko kaɗan sa'ad da suka ji labari, cewa wani ya zo domin ya inganta zaman lafiyar mutanen Isra'ila.

11. Da na iso Urushalima na yi kwana uku,

12. sai na fita da dare tare da waɗansu mutane kima,ban faɗa wa kowa abin da Allahna ya sa a zuciyata in yi wa Urushalima ba. Ba waɗansu dabbobi kuma tare da ni, sai dai dabbar da na hau.

13. Da na fita, sai na bi ta Ƙofar Kwari zuwa Rijiyar Dila da Ƙofar Juji, na dudduba garun Urushalima, wanda aka rushe, da ƙofofinsa da wuta ta cinye.

14. Na yi gaba zuwa Ƙofar Maɓuɓɓuga da Tafkin Sarki, amma dabbar da na hau ba ta sami wurin wucewa ba.

Karanta cikakken babi Neh 2