Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Sh 4:31-49 Littafi Mai Tsarki (HAU)

31. Ubangiji Allahnku, Allah mai jinƙai ne. Faufau, ba zai kunyata ku ba, ba kuwa zai hallaka ku ba, ba kuma zai manta da alkawarin da ya rantse wa kakanninku ba.

32. “Ku tambaya mana, ko a kwanakin dā kafin zamaninku, tun ma daga lokacin da Allah ya yi mutum a duniya, ku tantambaya daga wannan kusurwa ta samaniya zuwa waccan, ko wani babban abu irin wannan ya taɓa faruwa, ko kuma an taɓa jin labarin irinsa?

33. Akwai wata jama'a da ta taɓa jin muryar wani allah tana magana ta tsakiyar wuta kamar yadda kuka ji, har suka rayu?

34. Ko kuma, da akwai wani allah wanda ya taɓa ƙoƙarin fitar da al'umma saboda kansa daga cikin tsakiyar wata al'umma ta wurin wahalai, da alamu, da mu'ujizai, da yaƙi, da nuna iko, da babbar razana kamar yadda Ubangiji Allahnku ya yi dominku a ƙasar Masar a kan idonku duka?

35. An nuna muku wannan don ku sani Ubangiji shi ne Allah, banda shi, ba wani kuma.

36. Ya sa ku ji muryarsa daga Sama don ya horar da ku. Ya kuma sa ku ga babbar wutarsa a duniya, kuka kuma ji muryarsa daga cikin wutar.

37. Saboda ya ƙaunaci kakanninku shi ya sa ya zaɓi zuriyarsu a bayansu, shi kansa kuma ya fisshe ku daga Masar da ikonsa mai girma.

38. Ya kori al'ummai a gabanku waɗanda suka fi ku girma da iko, ya kawo ku a ƙasarsu, ya ba ku ita abar gādo kamar yadda yake a yau.

39. Domin haka, yau sai ku sani, ku kuma riƙe a zuciyarku, cewa Ubangiji shi kaɗai ne Allah a sama da duniya. Banda shi, ba wani kuma.

40. Sai ku kiyaye dokokinsa da umarnansa waɗanda na umarce ku da su yau, don zaman lafiyarku da na 'ya'yanku a bayanku, domin kuma ku yi tsawon rai a ƙasa wadda Ubangiji Allahnku yake ba ku har abada.”

41. Sai Musa ya keɓe birane uku a hayin gabashin Urdun,

42. domin wanda ya yi kisankai ya gudu zuwa can, wato wanda ya kashe mutum ba da niyya ba, babu kuma ƙiyayya tsakaninsu a dā. In ya gudu zuwa ɗaya daga cikin biranen zai tsirar da kansa.

43. Biranen su ne, Bezer cikin jeji a kan tudu domin Ra'ubainawa, da Ramot cikin Gileyad domin Gadawa, da Golan cikin Bashan domin Manassawa.

44. Waɗannan su ne dokokin da Musa ya ba Isra'ilawa,

45. su ne kalmomi, da dokoki, da farillai, waɗanda Musa ya faɗa wa jama'ar Isra'ila, bayan da sun fito Masar,

46. a hayin Urdun a kwari daura da Bet-feyor, a ƙasar Sihon, Sarkin Amoriyawa, mazaunan Heshbon, waɗanda Musa da Isra'ilawa suka ci da yaƙi sa'ad da suka fita daga ƙasar Masar.

47. Suka mallaki ƙasar Sihon, da ƙasar Og, Sarkin Bashan, sarakuna biyu na Amoriyawa waɗanda suke a hayin gabashin Urdun.

48. Ƙasar ta kama daga Arower wanda yake a kwarin kogin Arnon zuwa dutsen Siriyon, wato Harmon,

49. da dukan Araba a hayin gabashin Urdun, har zuwa tekun Araba a gindin gangaren Fisga.

Karanta cikakken babi M. Sh 4