Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Sh 3:13-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Sauran ƙasar Gileyad, da dukan ƙasar Bashan wadda take ƙarƙashin mulkin Og, wato dukan yankin ƙasar Argob.”(Duk dai yankin ƙasan nan wadda ake kira ƙasar Refayawa.) “Na ba da ita ga rabin kabilar Manassa.”

14. (Yayir na zuriyar Manassa ya karɓi dukan yankin ƙasar Argob a Bashan har zuwa iyakar Geshurawa da Ma'akatiyawa. Sai ya kira ƙauyukan wurin da sunansa, Hawot-yayir.)

15. “Na ba Makir Gileyad.

16. Na ba Ra'ubainawa da Gadawa yankin ƙasar da ta tashi daga Gileyad har zuwa kwarin Arnon, tsakiyar kwarin shi ne iyakar har zuwa kwarin kogin Yabbok wanda ya yi iyaka da Ammonawa.

17. Na kuma ba su Araba, Urdun shi ne iyaka daga Kinneret, har zuwa Tekun Araba, wato Tekun Gishiri, a gangaren gindin Dutsen Fisga wajen gabas.

18. “A wancan lokaci ne na yi muku umarni, na ce, ‘Ubangiji Allahnku ya ba ku wannan ƙasa, ku mallake ta. Dukan mayaƙanku za su haye da shirin yaƙi a gaban 'yan'uwanku, Isra'ilawa.

19. Amma matanku, da 'ya'yanku, da dabbobinku, na sani kuna da dabbobi da yawa, su ne za ku bari a garuruwan da na ba ku,

20. har lokacin da Ubangiji ya zaunar da 'yan'uwanku kamar yadda ya zamshe ku, su ma su mallaki ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba su a hayin Urdun, sa'an nan kowa zai koma ga mallakarsa.’

21. “A lokacin kuwa na umarci Joshuwa na ce, ‘Ai, da idonka ka ga dukan abin da Ubangiji Allahnku ya yi wa waɗannan sarakuna biyu. Haka nan kuwa Ubangiji zai yi wa mulkoki waɗanda za ku haye zuwa wurinsu.

Karanta cikakken babi M. Sh 3