Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Sh 2:23-37 Littafi Mai Tsarki (HAU)

23. Haka nan kuma ya faru da Awwiyawa mazaunan ƙauyukan da suke kewaye da Gaza, wato su Kaftorawa waɗanda suka zo daga Kaftor, suka hallakar da su, suka zauna a wurinsu.)

24. “Ubangiji ya ce, ‘Ku tashi, ku kama hanya, ku haye kwarin Arnon. Duba, na ba da Sihon Ba'amore, Sarkin Heshbon, da ƙasarsa a hannunku, ku fara mallakar ƙasar, ku yaƙe shi.

25. A wannan rana ce zan fara sa al'ummai ko'ina a duniya su razana, su ji tsoronku. Sa'ad da za su ji labarinku, za su yi rawar jiki, su damu ƙwarai.’ ”

26. “Sa'an nan na aiki manzanni daga jejin Kedemot zuwa Sihon, Sarkin Heshbon, ina neman zaman lafiya, na ce,

27. ‘Ka yardar mini in bi ta cikin ƙasarka. Zan bi ta kan babbar hanya sosai, ba zan ratse dama ko hagu ba.

28. Zan sayi abincin da zan ci, da ruwan da zan sha a wurinku.

29. Kai dai ka yardar mini in bi in wuce kamar yadda zuriyar Isuwa, mazaunan Seyir, da Mowabawa, mazaunan Ar, suka yardar mini. Gama ina so in haye Urdun zuwa ƙasa wadda Ubangiji Allahnmu yake ba mu.’

30. “Amma Sihon, Sarkin Heshbon, ya ƙi yarda mu wuce, gama Ubangiji Allahnku ya riga ya taurare hankalinsa da zuciyarsa don ya bashe shi a hannunku, kamar yadda yake a yau.

31. “Sai Ubangiji ya ce mini, ‘Duba, na fara ba da Sihon da ƙasarsa a gare ku. Ku fara fāɗa wa ƙasarsa da yaƙi don ku mallake ta.’

32. Sai Sihon da mutanensa suka fita su gabza yaƙi da mu a Yahaza.

33. Ubangiji Allahnmu ya bashe shi a hannunmu, muka ci nasara a kansa, da 'ya'yansa, da dukan mutanensa.

34. Muka ci dukan garuruwansa, muka hallaka kowane gari, da mata, da maza, da yara, ko ɗaya bai ragu ba.

35. Sai dabbobi ne kaɗai da dukiyar garuruwan da muka ci, su ne muka kwashe ganima.

36. Daga Arower wadda take gefen kwarin kogin Arnon, zuwa Gileyad har ma da garin da yake cikin kwarin, Ubangiji Allahnmu ya ba da dukan kome a gare mu. Ba birnin da ya gagare mu.

37. Amma ba ku kusaci ƙasar Ammonawa ba, wato ƙasar da take a kwarin kogin Yabbok, da garuruwan ƙasar tuddai, da wuraren da Ubangiji Allahnmu ya hana mu.”

Karanta cikakken babi M. Sh 2