Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Sh 2:16-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. “Sa'ad da dukan waɗanda suka isa yaƙi suka mutu,

17. sai Ubangiji ya yi mini magana, ya ce,

18. ‘Yau za ku ratsa kan iyakar ƙasar Mowab a Ar.

19. Sa'ad da ku kuka zo kusa da Ammonawa, kada ku dame su, ko ku tsokane su, gama ba zan ba ku abin mallaka daga yankin ƙasar Ammonawa ba, domin na ba da ita ta zama mallaka ga zuriya Lutu.’ ”

20. (Ita ma aka lasafta ta ƙasar Refayawa ce. Dā Refayawa waɗanda Ammonawa suke kira Zuzawa, su ne suka zauna cikinta.

21. Manyan mutane masu yawa dogaye ne kuma kamar Anakawa, amma Ubangiji ya hallakar da su a gabansu, suka kore su, suka zauna a wurinsu,

22. daidai kamar yadda Ubangiji ya yi wa zuriyar Isuwa waɗanda suka zauna a Seyir, sa'ad da ya hallakar da Horiyawa a gabansu. Su kuma suka kore su suka zauna a wurinsu har wa yau.

23. Haka nan kuma ya faru da Awwiyawa mazaunan ƙauyukan da suke kewaye da Gaza, wato su Kaftorawa waɗanda suka zo daga Kaftor, suka hallakar da su, suka zauna a wurinsu.)

24. “Ubangiji ya ce, ‘Ku tashi, ku kama hanya, ku haye kwarin Arnon. Duba, na ba da Sihon Ba'amore, Sarkin Heshbon, da ƙasarsa a hannunku, ku fara mallakar ƙasar, ku yaƙe shi.

25. A wannan rana ce zan fara sa al'ummai ko'ina a duniya su razana, su ji tsoronku. Sa'ad da za su ji labarinku, za su yi rawar jiki, su damu ƙwarai.’ ”

26. “Sa'an nan na aiki manzanni daga jejin Kedemot zuwa Sihon, Sarkin Heshbon, ina neman zaman lafiya, na ce,

27. ‘Ka yardar mini in bi ta cikin ƙasarka. Zan bi ta kan babbar hanya sosai, ba zan ratse dama ko hagu ba.

28. Zan sayi abincin da zan ci, da ruwan da zan sha a wurinku.

29. Kai dai ka yardar mini in bi in wuce kamar yadda zuriyar Isuwa, mazaunan Seyir, da Mowabawa, mazaunan Ar, suka yardar mini. Gama ina so in haye Urdun zuwa ƙasa wadda Ubangiji Allahnmu yake ba mu.’

Karanta cikakken babi M. Sh 2