Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Sh 16:6-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Amma ku miƙa ta a wurin da Ubangiji Allahnku zai zaɓa don ya tabbatar da sunansa. Nan za ku miƙa hadayar ƙetarewa da yamma da faɗuwar rana, daidai da lokacin da kuka fito daga Masar.

7. Sai ku dafa shi, ku ci a inda Ubangiji Allahnku zai zaɓa. Da safe sai ku koma alfarwanku.

8. Kwana shida za ku yi kuna cin abinci marar yisti, amma a rana ta bakwai sai ku yi muhimmin taro saboda Ubangiji Allahnku. Kada ku yi aiki a wannan rana.

9. “Sai ku ƙirga mako bakwai, wato ku fara ƙirga mako bakwai ɗin daga lokacin da kuka fara sa lauje don ku yanke hatsinku da suke tsaye.

10. Sa'an nan sai ku yi Idin Makonni domin Ubangiji Allahnku. Za ku ba da sadaka ta yardar rai gwargwadon albarkar da Ubangiji Allahnku ya sa muku.

11. Sai ku yi murna a gaban Ubangiji Allahnku a inda Ubangiji Allahnku ya zaɓa don ya tabbatar da sunansa, ku da 'ya'yanku mata da maza, da barorinku mata da maza, da Balawen da suke zaune a garinku, da baƙo, da maraya, da gwauruwa ta gaske, waɗanda suke zaune tare da ku.

12. Ku tuna fa, ku dā bayi ne a Masar, domin haka ku lura, ku kiyaye waɗannan dokoki.

13. “Za ku yi Idin Bukkoki kwana bakwai bayan da kun gama tattara amfaninku daga masussukanku, da wurin matsewar ruwan inabinku.

14. Sai ku yi murna a cikin idin, ku da 'ya'yanku mata da maza, da barorinku mata da maza, da Balawe, da baƙo, da maraya, da gwauruwa ta gaske, waɗanda suke zaune tare da ku.

15. Za ku kiyaye idin ga Ubangiji Allahnku har kwana bakwai a inda Ubangiji zai zaɓa, gama Ubangiji Allahnku zai yalwata dukan amfanin gonakinku, da dukan ayyukan hannunku don ku cika da murna.

Karanta cikakken babi M. Sh 16