Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Sh 16:1-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. “Ku kiyaye watan Abib don ku yi Idin Ƙetarewa ga Ubangiji Allahnku, gama a watan Abib ne Ubangiji Allahnku ya fito da ku daga Masar da dad dare.

2. Sai ku miƙa hadayar ƙetarewa daga garkenku na tumaki da na shanu ga Ubangiji Allahnku a wurin da Ubangiji ya zaɓa domin ya tabbatar da sunansa.

3. Kada ku ci abinci mai yisti tare da hadayar. Kwana bakwai za ku riƙa cin abinci marar yisti tare da hadayar, gama abincin wahala ne, gama da gaggawa kuka fita daga ƙasar Masar, don haka za ku tuna da ranar da kuka fito daga ƙasar Masar dukan kwanakinku.

4. Kada a iske yisti a ƙasarku duka har kwana bakwai. Kada kuma ku ajiye naman hadayar da kuka miƙa da yamma a rana ta fari ya kwana har safiya.

5. “Kada ku miƙa hadayar ƙetarewa a kowane garin da Ubangiji Allahnku yake ba ku.

6. Amma ku miƙa ta a wurin da Ubangiji Allahnku zai zaɓa don ya tabbatar da sunansa. Nan za ku miƙa hadayar ƙetarewa da yamma da faɗuwar rana, daidai da lokacin da kuka fito daga Masar.

7. Sai ku dafa shi, ku ci a inda Ubangiji Allahnku zai zaɓa. Da safe sai ku koma alfarwanku.

8. Kwana shida za ku yi kuna cin abinci marar yisti, amma a rana ta bakwai sai ku yi muhimmin taro saboda Ubangiji Allahnku. Kada ku yi aiki a wannan rana.

9. “Sai ku ƙirga mako bakwai, wato ku fara ƙirga mako bakwai ɗin daga lokacin da kuka fara sa lauje don ku yanke hatsinku da suke tsaye.

10. Sa'an nan sai ku yi Idin Makonni domin Ubangiji Allahnku. Za ku ba da sadaka ta yardar rai gwargwadon albarkar da Ubangiji Allahnku ya sa muku.

11. Sai ku yi murna a gaban Ubangiji Allahnku a inda Ubangiji Allahnku ya zaɓa don ya tabbatar da sunansa, ku da 'ya'yanku mata da maza, da barorinku mata da maza, da Balawen da suke zaune a garinku, da baƙo, da maraya, da gwauruwa ta gaske, waɗanda suke zaune tare da ku.

12. Ku tuna fa, ku dā bayi ne a Masar, domin haka ku lura, ku kiyaye waɗannan dokoki.

Karanta cikakken babi M. Sh 16