Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Mah 9:9-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Amma itacen zaitun ya ce musu, ‘In bar maina wanda da shi ake girmama alloli da mutane, don in tafi in yi ta fama da itatuwa?’

10. Sai kuma itatuwa suka ce wa itacen ɓaure, ‘Ka zo, ka zama sarkinmu.’

11. Amma itacen ɓaure ya ce musu, ‘In bar kyawawan 'ya'yana masu zaƙi, don in tafi in yi ta fama da itatuwa?’

12. Itatuwa kuma suka ce wa kurangar inabi, ‘Ki zo, ki mallake mu.’

13. Sai kurangar inabi ta ce, ‘In bar ruwan inabina wanda yake faranta zuciyar allolin da ta mutane, don in tafi, in yi ta fama da itatuwa?’

14. Sa'an nan dukan itatuwa suka ce wa itacen ƙaya, ‘Ka zo, ka zama sarkinmu.’

15. Itacen ƙaya kuwa ya ce wa itatuwan, ‘In da gaske kuke, kuna so ku naɗa ni sarkinku, to, sai ku zo, ku fake a inuwata, in ba haka ba kuwa, bari wuta ta fito daga itacen ƙaya ta cinye itacen al'ul na Lebanon.’ ”

16. Yotam ya ci gaba da cewa, “Yanzu kun naɗa Abimelek sarki da zuciya ɗaya ke nan? Kun yi wa Yerubba'al da iyalinsa daidai ke nan? Wannan ne abin da ya cancance shi?

17. Ku tuna fa mahaifina ya yi yaƙi dominku. Ya kasai da ransa domin ya cece ku daga Madayanawa.

18. Amma ga shi, yau kun juya kuna gāba da gidan mahaifina. Kun kashe 'ya'yansa maza, su saba'in, a dutse guda, kuka naɗa Abimelek, ɗan da baiwa ta haifa, ya zama sarki a Shekem, don dai kawai shi ɗan'uwanku ne.

19. Yanzu dai idan abin da kuka yi wa Yerubba'al da iyalinsa daidai ne, to, sai ku yi farin ciki da Abimelek, ku sa shi kuma ya ji daɗinku.

20. Amma idan ba haka yake ba, Allah ya sa wuta ta fito daga wurin Abimelek ta cinye mutanen Shekem da na Bet-millo. Bari Allah ya sa kuma wuta ta fito daga wurin mutanen Shekem da na Bet-millo ta cinye Abimelek.”

21. Sa'an nan Yotam ya tsere. Ya tafi ya zauna a Biyer, gama yana tsoron ɗan'uwansa Abimelek.

22. Abimelek kuwa ya yi shekara uku, yana mulkin Isra'ila.

23. Ubangiji kuma ya sa husuma ta tashi tsakanin Abimelek da mutanen Shekem. Shugabannin Shekem kuwa suka tayar masa.

24. Wannan ya faru domin a ɗauki fansar jinin, 'ya'yan Yerubba'al, maza, su saba'in, a kan Abimelek ɗan'uwansu, wanda ya kashe su, da kuma a kan shugabannin Shekem, waɗanda suka taimake shi ya kashe 'yan'uwansa.

25. Shugabannin Shekem kuwa suka sa mutane su yi kwanto a kan dutwatsu gāba da Abimelek. Suka yi wa duk wanda ya bi ta wannan hanya fashi. Sai aka faɗa wa Abimelek.

Karanta cikakken babi L. Mah 9