Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Mah 4:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Bayan rasuwar Ehud, Isra'ilawa suka sāke yin zunubi a gaban Ubangiji.

2. Ubangiji kuwa ya yarda Yabin Sarkin Kan'ana, wanda yake mulkin Hazor ya ci su da yaƙi. Sisera, wanda yake zaune a Haroshet ta al'ummai, shi ne shugaban sojojin Yabin.

3. Sa'an nan jama'ar Isra'ila suka yi kuka ga Ubangiji suna neman taimako, gama Yabin yana da karusai ɗari tara na ƙarfe, ya kuma tsananta wa Isra'ilawa, ya mugunta musu shekara ashirin. Isra'ilawa kuwa suka yi kuka ga Ubangiji domin ya taimake su.

4. Debora, matar Lafidot, ita ce annabiya. Tana hukuncin Isra'ilawa.

5. Ta zauna a gindin giginyar Debora tsakanin Rama da Betel, a ƙasar tudu ta Ifraimu. Isra'ilawa sukan haura zuwa wurinta don ta yi musu shari'a.

6. Sai ta aika a kirawo Barak, ɗan Abinowam, daga birnin Kedesh a ƙasar Naftali. Ta ce masa, “Ubangiji Allah na Isra'ila ya ba ka wannan umarni, ya ce, ‘Ka tafi ka tara mutanenka a Dutsen Tabor, ka kuma ɗauki mutum dubu goma (10,000), daga kabilar Naftali da ta Zabaluna.

7. Ni kuwa zan jawo Sisera, shugaban sojojin Yabin, da karusansa, da ƙungiyoyin sojojinsa ya yi karo da kai a Kogin Kishon, zan kuwa bashe shi a hannunka.’ ”

8. Barak ya ce mata, “Idan za ki tafi tare da ni, zan tafi, amma idan ba za ki tafi tare da ni ba, ni ma ba zan tafi ba.”

Karanta cikakken babi L. Mah 4