Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Mah 20:29-44 Littafi Mai Tsarki (HAU)

29. Isra'ilawa kuwa suka sa 'yan kwanto kewaye da Gibeya.

30. Sa'an nan suka tafi su kara da mutanen Biliyaminu a rana ta uku. Suka jā dāgar yaƙi gaba da Gibeya kamar dā.

31. Mutanen Biliyaminu kuma suka fito, suka tasar musu. Aka jawo su nesa da birnin. Suka fara kashe Isra'ilawa kamar yadda suka yi a dā, suka kashe wajen mutum talatin a kan karauka wadda ta nufi Betel da wadda ta nufi Gibeya, da filaye.

32. Sai mutanen Biliyaminu suka ce, “Mun fatattake su kamar dā.”Amma Isra'ilawa suka ce, “Mu gudu don mu jawo su nesa da birnin zuwa karauka.”

33. Isra'ilawa duka suka tashi daga wurin da suke, suka jā dāga a Ba'altamar. Mutanensu da suke kwanto a yammacin Gibeya suka fito.

34. Horarrun sojojin Isra'ila, su dubu goma (10,000), suka faɗa wa Gibeya. Yaƙi kuwa ya yi zafi, amma mutanen Biliyaminu ba su san masifa tana gab da su ba.

35. Ubangiji kuwa ya fatattake mutanen Biliyaminu a gaban Isra'ilawa. Isra'ilawa kuwa suka hallaka mutanen Biliyaminu dubu ashirin da biyar da ɗari ɗaya (25,100) a wannan rana, waɗannan duka kuwa mayaƙa ne.

36. Mutanen Biliyaminu kuwa suka gane an ci su da yaƙi.Mutanen Isra'ila kuwa suka yi ta ja da baya daga mutanen Biliyaminu domin sun dogara ga mutanensu da suka yi wa Gibeya kwanto.

37. Sai 'yan kwanto suka gaggauta suka faɗa wa Gibeya, suka kutsa suka kashe dukan waɗanda suke a birnin.

38. Alamar da mayaƙan Isra'ila da na 'yan kwantonsu suka daidaita a tsakaninsu, ita ce murtukewar hayaƙi a cikin birnin.

39. Idan mutanen Isra'ila sun hangi hayaƙin, sai su juya su fāɗa wa mutanen Biliyaminu da yaƙi. Kafin alamar hayaƙin sai mutanen Biliyaminu suka fara kashe wa Isra'ilawa wajen mutum talatin. Suka ce, “Ai, suna shan ɗibga a hannunmu kamar yadda suka sha da fari.”

40. Amma sa'ad da alamar hayaƙin ta fara murtukewa a cikin birnin, sai mutanen Biliyaminu suka juya, suka duba, suka ga hayaƙi ya murtuke cikin birnin, ya yi sama.

41. Da mutanen Isra'ila suka juyo kansu, sai mutanen Biliyaminu suka tsorata, gama sun ga masifa ta auko musu.

42. Don haka suka juya suka kama gudu suka nufi hamada, amma ba su tsira ba. Aka datse su tsakanin 'yan kwanto da sauran sojojin Isra'ilawa.

43. Suka yi wa mutanen Biliyaminu tarko, suka runtume su ba tsayawa tun daga Menuha har zuwa daura da Gibeya daga gabas.

44. Aka kashe jarumawan mutanen Biliyaminu mutum dubu goma sha takwas (18,000).

Karanta cikakken babi L. Mah 20