Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Mah 20:20-36 Littafi Mai Tsarki (HAU)

20. Suka kuwa fita su yi yaƙi da mutanen Biliyaminu, suka jā dāgar yaƙi suna fuskantar Gibeya.

21. Mutanen Biliyaminu kuwa suka fito daga birnin suka hallakar da mutum dubu ashirin da biyu (22,000), daga cikin mutanen Isra'ila a ranar.

22-23. Mutanen Isra'ila suka tafi inda ake sujada suka yi makoki a gaban Ubangiji har zuwa dare. Suka tambaye shi suka ce, “Mu sāke zuwa domin mu yi yaƙi da 'yan'uwanmu mutanen Biliyaminu?”Ubangiji ya ce musu, “I, ku tafi.”Saboda haka sai sojojin Isra'ilawa suka ƙarfafa, suka sāke jān dāga a inda suka jā ta dā.

24. Sai mutanen Isra'ila suka tafi su kara da mutanen Biliyaminu a rana ta biyu.

25. Mutanen Biliyaminu kuwa suka fito daga birnin suka hallakar da mutum dubu goma sha takwas (18,000) daga cikin Isra'ilawa. Dukan waɗannan da aka hallaka horarru ne.

26. Dukan rundunan Isra'ilawa suka haura zuwa Betel, suka yi makoki, suka zauna a gaban Ubangiji suka yi azumi har maraice. Sa'an nan suka miƙa wa Ubangiji hadayu na ƙonawa da na salama.

27-28. Suka sāke yin tambaya ga Ubangiji suka ce, “Mu sāke tafiya mu yi yaƙi da 'yan'uwanmu, mutanen Biliyaminu, ko kuwa mu bari?”Ubangiji kuwa ya ce musu, “Ku je, gama gobe zan ba da su gare ku.” A lokacin nan akwatin alkawari na Ubangiji yana nan. Finehas ɗan Ele'azara, ɗan Haruna, shi ne mai aiki a gabansa.

29. Isra'ilawa kuwa suka sa 'yan kwanto kewaye da Gibeya.

30. Sa'an nan suka tafi su kara da mutanen Biliyaminu a rana ta uku. Suka jā dāgar yaƙi gaba da Gibeya kamar dā.

31. Mutanen Biliyaminu kuma suka fito, suka tasar musu. Aka jawo su nesa da birnin. Suka fara kashe Isra'ilawa kamar yadda suka yi a dā, suka kashe wajen mutum talatin a kan karauka wadda ta nufi Betel da wadda ta nufi Gibeya, da filaye.

32. Sai mutanen Biliyaminu suka ce, “Mun fatattake su kamar dā.”Amma Isra'ilawa suka ce, “Mu gudu don mu jawo su nesa da birnin zuwa karauka.”

33. Isra'ilawa duka suka tashi daga wurin da suke, suka jā dāga a Ba'altamar. Mutanensu da suke kwanto a yammacin Gibeya suka fito.

34. Horarrun sojojin Isra'ila, su dubu goma (10,000), suka faɗa wa Gibeya. Yaƙi kuwa ya yi zafi, amma mutanen Biliyaminu ba su san masifa tana gab da su ba.

35. Ubangiji kuwa ya fatattake mutanen Biliyaminu a gaban Isra'ilawa. Isra'ilawa kuwa suka hallaka mutanen Biliyaminu dubu ashirin da biyar da ɗari ɗaya (25,100) a wannan rana, waɗannan duka kuwa mayaƙa ne.

36. Mutanen Biliyaminu kuwa suka gane an ci su da yaƙi.Mutanen Isra'ila kuwa suka yi ta ja da baya daga mutanen Biliyaminu domin sun dogara ga mutanensu da suka yi wa Gibeya kwanto.

Karanta cikakken babi L. Mah 20