Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Mah 13:8-15-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Sa'an nan Manowa ya yi roƙo ga Ubangiji ya ce, “Ya Ubangijina, ina roƙonka ka bar mutumin Allah wanda ka aiko, ya sāke zuwa wurinmu, ya faɗa mana abin da za mu yi wa yaron da za a haifa.”

9. Allah kuwa ya ji roƙon Manowa, ya sāke aiko da mala'ikansa wurin matar, sa'ad da take a saura, mijinta kuwa ba ya tare da ita.

10. Don haka sai ta sheƙa a guje zuwa wurin mijinta, ta faɗa masa, “Ga mutumin da ya zo wurina ran nan, ya sāke zuwa.”

11. Manowa fa ya tashi ya tafi tare da ita. Da ya zo wurin mutumin, sai ya tambaye shi, “Kai ne mutumin da ya yi magana da macen nan?”Sai ya amsa ya ce, “Ni ne.”

12. Manowa kuma ya ce, “Lokacin da maganarka ta cika, wane irin yaro ne zai zama, me kuma za mu yi?”

13. Mala'ikan Ubangiji ya amsa, ya ce wa Manowa, “Sai matarka ta kiyaye dukan abin da na faɗa mata.

14. Kada ta ci kowane irin abu da aka yi da inabi, kada kuma ta sha ruwan inabi ko abin sa maye. Kada ta ci haramtaccen abu, amma ta kiyaye dukan abin da na umarce ta.”

15-16. Manowa dai bai san mala'ikan Ubangiji ne ba, sai ya ce wa mala'ikan, “Ina roƙonka ka jira, mu yanka maka ɗan akuya.”Amma mala'ikan ya ce masa, “Ko na jira ba zan ci abincinku ba, amma idan kana so ka yanka, sai ka shirya hadayar ƙonawa, ka miƙa ta ga Ubangiji.”

Karanta cikakken babi L. Mah 13