Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 22:26-37 Littafi Mai Tsarki (HAU)

26. Mala'ikan Ubangiji kuma ya sha kanta, ya tsaya a ƙunƙuntaccen wuri inda ba wurin juyawa zuwa dama ko hagu.

27. Da jakar ta ga mala'ikan Ubangiji, sai ta kwanta a ƙafafun Bal'amu. Sai Bal'amu ya husata, ya bugi jakar da sandansa.

28. Ubangiji kuwa ya buɗe bakin jakar, ta ce wa Bal'amu, “Me na yi maka, da ka buge ni har sau uku?”

29. Bal'amu ya ce mata, “Domin kin shashantar da ni, da a ce ina da takobi a hannuna, da na kashe ki.”

30. Sai jakar ta ce wa Bal'amu, “Ba ni ce jakarka ba wadda kake ta hawa dukan lokacin nan har zuwa yau? Na taɓa yi maka haka?”Ya ce, “A'a.”

31. Ubangiji kuwa ya buɗe idanun Bal'amu, ya ga mala'ikan Ubangiji yana tsaye a hanya da takobi zāre a hannunsa. Sai ya sunkuyar da kansa, ya fāɗi rubda ciki.

32. Mala'ikan Ubangiji kuwa ya ce masa, “Me ya sa ka bugi jakarka har sau uku? Na fito ne don inhana ka, gama hanyarka ba daidai ba ce a gabana.

33. Jakar ta gan ni, ta kauce mini har sau uku. Da ba ta kakuce mini ba, lalle da na kashe ka, in bar ta da rai.”

34. Sai Bal'amu ya ce wa mala'ikan Ubangiji, “Na yi zunubi, gama ban sa ka tsaya a hanya don ka tarye ni ba. Yanzu fa, idan ka ga mugun abu ne, to, sai in koma.”

35. Ubangiji kuwa ya ce wa Bal'amu, “Tafi tare da mutanen, amma abin da na faɗa maka shi kaɗai za ka faɗa.” Sai Bal'amu ya tafi tare da dattawan Balak.

36. Sa'ad da Balak ya ji Bal'amu ya zo, sai ya fito ya tarye shi a Ar, wato wani birni a bakin Kogin Arnon, a kan iyakar Mowab.

37. Sai Balak ya ce wa Bal'amu, “Ashe, ban aika a kirawo ka ba? Me ya sa ba ka zo wurina ba, sai yanzu? Ko ban isa in ɗaukaka ka ba ne?”

Karanta cikakken babi L. Kid 22