Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Fir 23:21-38 Littafi Mai Tsarki (HAU)

21. A ranar fa za su yi shela don a yi muhimmin taro. Ba za su yi aiki mai wuya ba. Wannan doka ce gare su har abada a inda suke duka.

22. Sa'ad da suka girbe amfanin gonakinsu, ba za su girbe har da gyaffan gonakinsu ba, ba kuma za su yi kalar amfanin gonakinsu ba. Za su bar wa matalauta da baƙi. Shi ne Ubangiji Allahnsu.

23. Ubangiji ya yi magana da Musa, cewa,

24. ya ce wa Isra'ilawa su mai da rana ta fari ga wata na bakwai ta zama ranar hutu musamman, sa'ad da za su ji busar ƙaho, sai su taru domin yin sujada.

25. Ba za su yi aiki mai wuya ba. Za su miƙa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji.

26. Ubangiji ya yi magana da Musa, cewa,

27. rana ta goma ga watan bakwai za ta zama rana ta yin kafara da lokacin yin muhimmin taro. Kada su ci abinci a ranar, su taru su yi sujada, su miƙa hadaya taƙonawa ga Ubangiji.

28. Ba za su yi aiki a wannan rana ba, gama rana ce ta yin kafara dominsu.

29. Duk wanda ya ci abinci a wannan rana ba za a lasafta shi ɗaya daga cikin jama'ar Allah ba.

30. Duk kuma wanda ya yi aiki a wannan rana, Ubangiji kansa zai kashe shi.

31. Wannan ka'ida ta shafi dukan zuriyarsu a duk inda suke.

32. Daga faɗuwar ranar tara ga watan, har zuwa faɗuwar ranar goma ga watan, su kiyaye wannan ta zama ranar hutu musamman. A wannan lokaci ba wanda zai ci abinci.

33. Ubangiji kuma ya yi magana da Musa, ya ce ya faɗa wa Isra'ilawa, cewa,

34. a rana ta goma sha biyar ga watan bakwai za a yi Idin Bukkoki kwana bakwai saboda Ubangiji.

35. Za a yi muhimmin taro na sujada a rana ta fari. Ba za su yi aiki ba.

36. A kwana bakwai ɗin za su riƙa miƙa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji. A rana ta takwas kuma sai su yi muhimmin taro na sujada, su miƙa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji. Rana ce ta yin sujada, kada su yi aiki.

37. Waɗannan su ne ƙayyadaddun idodi na Ubangiji da za su riƙa yi domin sujada. Za su miƙa hadayu ga Ubangiji, wato, hadaya ta ƙonawa, da hadaya ta gari, da ta sadakoki, da hadayu na sha. Za a miƙa kowace hadaya a ranarta.

38. Waɗannan idodi ƙari ne a kan lokatan sujada da aka saba, hadayun kuma ƙari ne a kan kyautan da aka saba bayarwa, kamar su hadaya don cika wa'adi, da hadaya ta yardar rai da suke bayarwa ga Ubangiji.

Karanta cikakken babi L. Fir 23