Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Fir 19:3-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Sai ko wannenku ya girmama mahaifiyarsa da mahaifinsa, ya kuma kiyaye lokatan sujada. Ni ne Ubangiji Allahnku.

4. “Kada ku juya ku bi gumaka, ko kuma ku yi wa kanku gumaka na zubi. Ni ne Ubangiji Allahnku.

5. “Sa'ad da za ku miƙa hadaya ta salama ga Ubangiji, ku miƙa ta domin a karɓe ku.

6. A cinye ta a ranar da kuka miƙa ta ko kuwa kashegari. Abin da ya ragu har kwana na uku, sai a ƙone da wuta,

7. gama ta zama abar ƙyama, idan aka ci ta a rana ta uku, ba za ta zama abar karɓa ba.

8. Wanda ya ci ta a rana ta uku ɗin, zai zama da laifi, domin ya tozartar da abu mai tsarki na Ubangiji, sai a raba wannan mutum da jama'a.

9. “Sa'ad da kuke girbin amfanin ƙasarku, kada ku girbe gefen gonakinku, kada kuma ku yi kala bayan da kuka gama girbi.

10. Kada ku girbe kalar gonar inabinku, kada kuma ku tattara 'ya'yan inabinku da suka kakkaɓe, sai ku bar wa matalauta, da baƙo. Ni ne Ubangiji Allahnku.

11. “Kada ku yi sata, ko ku cuci wani, ko ku yi ƙarya.

12. Kada ku yi alkawari da sunana idan dai ba ku da niyyar cika shi, wannan zai jawo wa sunana ƙasƙanci. Ni ne Ubangiji Allahnku.

13. “Kada ku zalunci kowa ko ku yi masa ƙwace. Kada kuma ku bar lokacin biyan hakkin ma'aikaci ya kai har gobe.

14. Kada ku zagi kurma, kada kuma ku sa wa makaho abin tuntuɓe, amma ku ji tsoron Ubangiji Allahnku. Ni ne Ubangiji.

15. “Ku yi gaskiya da adalci cikin shari'a, kada ku ma ku yi wa matalauci son zuciya, ko ku goyi bayan mawadaci.

16. Kada ku yi ta yaɗa ƙarya game da wani. Sa'ad da wani yake cikin shari'ar kuɓutar da ransa, ku yi magana muddin dai shaidarku za ta taimake shi. Ni ne Ubangiji.

17. “Kada wani ya riƙe ɗan'uwansa da ƙiyayya a zuciyarsa, amma ya daidaita rashin jituwa da shi, don kada ya yi zunubi saboda shi.

Karanta cikakken babi L. Fir 19