Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Fir 13:45-58 Littafi Mai Tsarki (HAU)

45. Mai kuturta zai sa yagaggun tufafinsa, ya bar gashin kansa ba gyara, sa'an nan ya rufe leɓensa na sama, ya ta da murya, ya riƙa cewa, “Marar tsarki, marar tsarki.”

46. Muddin yana da cutar, zai zama marar tsarki. Zai zauna shi kaɗai a bayan zango.

47. Idan ana tsammani akwai cutar kuturta a rigar ulu ko ta lilin,

48. ko a tariyar zaren, ko a waɗari, ko a lilin, ko a ulu, ko a cikin fata, ko cikin kowane abu da aka yi da fata,

49. idan cutar ta zama kore-kore, ko jaja-jaja a rigar, ko a fatar, ko a tariyar zaren, ko a waɗarin, ko a kan abin da aka yi da fata, wannan cuta kuturta ce, sai a nuna wa firist.

50. Firist zai dudduba cutar, ya ajiye abin da yake da cutar har kwana bakwai.

51. A rana ta bakwai ɗin zai sāke dudduba cutar, idan cutar ta yaɗu a rigar, ko a tariyar zaren, ko a waɗarin, ko a fatar, komene ne za a yi da fata, wannan cuta muguwar kuturta ce, abin zai zama marar tsarki.

52. Zai ƙone rigar, ko tariyar zaren, ko waɗari na ulu ko na lilin, ko abin da dai aka yi da fata wanda yake da cutar, gama muguwar kuturta ce.

53. Amma idan firist ya dudduba ya ga cutar ba ta yaɗu a rigar, ko a tariyar zaren, ko a waɗarin, ko a abin da aka yi da fata ba,

54. sai firist ya umarta a wanke abin da yake da cutar, ya sāke ajiye shi har kwana bakwai kuma.

55. Firist kuma zai sāke duban abin da yake da cutar bayan da aka wanke shi, idan ya ga launin cutar bai sāke ba, ko da cutar ba ta yaɗu ba, abin ya zama marar tsarki ne nan, sai a ƙone shi da wuta, ko tabon cutar yana cikin abin ne, ko a waje.

56. Amma idan firist ɗin ya duba ya ga tabon ya dushe bayan da aka wanke shi, sai ya kece wurin daga fatar, ko tariyar zaren, ko waɗarin.

57. Idan tabon ya sāke bayyana kuma a rigar, ko a tariyar zaren, ko a waɗarin, ko a kan abin da aka yi da fata, ya yaɗu, sai a ƙone abin da yake da kuturtar.

58. Amma da rigar, ko a tariyar zaren, ko a waɗarin, ko kowane abin da aka yi da fata, wanda cutar ta wanku daga shi sa'ad da aka wanke, sai a sāke wanke shi, ya kuwa zama tsarkakakke ke nan.

Karanta cikakken babi L. Fir 13