Mai kuturta zai sa yagaggun tufafinsa, ya bar gashin kansa ba gyara, sa'an nan ya rufe leɓensa na sama, ya ta da murya, ya riƙa cewa, “Marar tsarki, marar tsarki.”