Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Josh 7:6-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Sai Joshuwa ya yayyage tufafinsa, ya faɗi rubda ciki a gaban akwatin Ubangiji har yamma. Shi da dattawan Isra'ila, suka zuba ƙura a bisa kansu.

7. Joshuwa ya ce, “Kaitonmu, ya Ubangiji Allah, me ya sa ka haye da jama'an nan zuwa wannan hayin Urdun, don ka bashe mu a hannun Amoriyawa, su hallakar da mu? Da ma mun haƙura, mun yi zamanmu a wancan hayin Urdun.

8. Ya Ubangiji, me zan ce bayan da Isra'ilawa sun ba da baya ga abokan gābansu?

9. Gama Kan'aniyawa da dukan mazaunan ƙasar za su ji labari, su kewaye mu, su shafe sunanmu daga duniya, to, me za ka yi don sunanka mai girma?”

10. Ubangiji kuwa ya ce wa Joshuwa, “Tashi, don me ka fāɗi rubda ciki?

11. Isra'ilawa sun yi zunubi. Sun ta da alkawarina, wanda na umarce su, gama sun ɗiba daga cikin abubuwan da aka haramta, sun sa a kayansu, sun yi ƙarya.

12. Saboda haka Isra'ilawa ba su iya tsayawa a gaban abokan gābansu ba, sun ba da baya ga abokan gābansu, gama sun zama haramtattu don hallakarwa. Daɗai, ba zan kasance tare da ku ba, sai dai kun kawar da haramtattun abubuwa da suke cikinku.

13. Tashi, ka tsarkake jama'a, ka ce, ‘Ku tsarkake kanku domin gobe, gama Ubangiji, Allah na Isra'ila ya ce akwai haramtattun abubuwa a tsakiyarku. Ya Isra'ila, ba ku iya tsayawa a gaban abokan gābanku ba, sai kun kawar da haramtattun abubuwa daga tsakiyarku.

14. Da safe kuwa za a gabatar da ku kabila kabila, zai zama kuwa kabilar da Ubangiji ya ware, za a gabatar da ita iyali iyali, iyalin da Ubangiji ya ware kuma, za a gabatar da su gida gida, gidan kuma da Ubangiji ya ware, za a gabatar da su mutum mutum.

15. Zai zama kuwa wanda aka same shi da haramtattun abubuwa, za a ƙone shi da wuta, shi da dukan abin da yake da shi, domin ya tā da alkawarin Ubangiji, ya kuma yi abin kunya cikin Isra'ila.’ ”

16. Joshuwa kuwa ya tashi da sassafe, ya gabatar da Isra'ilawa kabila kabila, aka ware kabilar Yahuza.

17. Ya gabatar da iyalan Yahuza, aka ware iyalin Zera. Ya gabatar da iyalin Zera gida gida, aka ware gidan Zebdi.

18. Ya gabatar da iyalin gidansa mutum mutum, aka ware Akan, ɗan Karmi, ɗan Zabdi, ɗan Zera na kabilar Yahuza.

19. Sai ya ce wa Akan, “Ɗana, ka ba da girma ga Ubangiji, Allah na Isra'ila, ka yabe shi ka gaya mini abin da ka yi, kada ka ɓoye mini.”

20. Akan kuwa ya amsa wa Joshuwa, ya ce, “A gaskiya kam, na yi wa Ubangiji, Allah na Isra'ila zunubi. Ga abin da na yi.

Karanta cikakken babi Josh 7