Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 7:3-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Ubangiji ya ce wa Ishaya, “Ka ɗauki ɗanka Sheyar-yashub ka je ka sami sarki Ahaz. Za ka same shi a hanya inda masu wankin tufafi suke aiki, a wajen ƙarshen wuriyar da yake kawo ruwa daga kududdufin da yake sama da ita.

4. Faɗa masa ya zauna da shiri, ya natsu, kada ya ji tsoro ko ya damu. Fushin sarki Rezin da Suriyawansa da na sarki Feka ba wani abu mai hatsari ba ne, bai fi hayaƙin 'yan ƙirare biyu da suke cin wuta ba.

5. Suriya tare da Isra'ila da sarkinta sun ƙulla maƙarƙashiya.

6. Nufinsu su kai wa ƙasar Yahuza yaƙi, su tsoratar da jama'a, don su haɗa kai da su, sa'an nan su naɗa ɗan Tabeyel.

7. “Amma ni Ubangiji na hurta, faufau wannan ba zai faru ba.

8. Don me? Saboda Dimashƙu ita ce ƙarfin Suriya, sarki Rezin kuwa shi ne ƙarfin Dimashƙu. Isra'ila kuwa a shekara sittin da biyar masu zuwa za ta karkasu, har ba za ta iya rayuwa ta zama al'umma ba.

9. Samariya ita ce ƙarfin Isra'ila, sarki Feka kuma shi ne ƙarfin Samariya.“Idan bangaskiyarku ba ta da ƙarfi, to, ba za ku dawwama ba.”

10. Ubangiji ya aika wa Ahaz da wani jawabi, ya ce,

11. “Ka roƙi Ubangiji Allahnka ya ba ka alama. Yana yiwuwa daga can zurfin lahira ne, ko kuma daga can cikin sama ne.”

12. Ahaz ya amsa, ya ce, “Ba zan nemi wata alama ba. Ba zan jarraba Ubangiji ba.”

13. Ga amsar da Ishaya ya ba Ahaz, “Kasa kunne yanzu, kai zuriyar sarki Dawuda. Ba abin kirki kuke yi ba, da kuka ƙure haƙurin jama'a, haƙurin Allah kuma kuke so ku ƙure?

14. Yanzu fa, Ubangiji kansa zai ba ku alama. Wata budurwa wadda take da ciki, za ta haifi ɗa, za a raɗa masa suna Immanuwel.

15. In ya yi girma har ya isa yanke shawara don kansa, madara da zuma ne abincinsa.

16. Kafin lokacin ya yi, ƙasashen sarakunan nan biyu waɗanda suka firgita ku za su zama kango.

17. “Ubangiji zai aukar maka da kwanakin wahala, kai da jama'arka, da dukan iyalin gidan sarauta, waɗanda suka fi muni tun lokacin da aka raba mulkin Isra'ila daga na Yahuza. Zai kawo Sarkin Assuriya!

18. “A lokacin nan, Ubangiji zai yi feɗuwa ya kirawo Masarawa su zo kamar ƙudaje daga manisantan mazaunan Kogin Nilu, ya kuma kirawo Assuriyawa su zo daga ƙasarsu kamar ƙudajen zuma.

19. Za su zo jingim su mamaye kwazazzabai da kogwanni cikin duwatsu, za su rufe kowane fili mai ƙayayuwa da kowace makiyaya.

Karanta cikakken babi Ish 7