Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 65:10-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Za su yi mini sujada, za su kai tumakinsu da shanunsu wurin kiwo a kwarin Sharon a wajen yamma, da kuma a kwarin Akor a wajen gabas.

11. “Amma ba haka zai zama ba, ga ku da kuka rabu da ni, ku waɗanda kuka yi watsi da Sihiyona, tsattsarkan dutsena, kuka yi sujada ga Gad da Meni, wato allolin sa'a da na ƙaddara.

12. Mutuwa ta ƙarfi da yaji za ku yi, gama sa'ad da na yi kiranku ba ku amsa ba, ba ku kasa kunne ba kuwa sa'ad da nake magana da ku. Kuka zaɓa ku yi mini rashin biyayya, ku kuma aikata mugunta.

13. Saboda haka ina faɗa muku, cewa su waɗanda suke yin sujada gare ni suna kuwa yi mini biyayya, za su sami wadataccen abinci da abin sha, amma ku za ku sha yunwa da ƙishi. Su za su yi murna, amma ku za ku sha kunya.

14. Za su raira waƙa don farin ciki, amma ku za ku yi kuka da karayar zuci.

15. Zaɓaɓɓun mutane ne za su mori sunayenku wajen la'antarwa. Ni, Ubangiji, zan kashe ku. Amma zan ba da sabon suna ga waɗanda suke yi mini biyayya.

16. Dukan wanda yake so ya roƙi albarka, sai ya roƙi Allah ya sa masa albarka, Allah da yake mai aminci ne. Dukan wanda zai sha rantsuwa, sai ya rantse da sunan Allah, Allah da yake mai aminci ne. Wahalan dā za su ƙare, za a kuwa manta da su.”

17. Ubangiji ya ce, “Ina yin sabuwar duniya da sabon sararin sama. Abubuwa na dā za a manta da su ɗungum.

18. Ku yi murna da farin ciki a kan abin da na halitta. Sabuwar Urushalima da nake halittawa za ta cika da murna, jama'arta kuma za su yi farin ciki.

19. Ni kaina kuma zan cika da murna saboda Urushalima da jama'arta. Ba kuka a can, ba bukatar neman taimako.

20. Jarirai ba za su mutu tun suna jarirai ba, ko wanne zai cika yawan kwanakinsa kafin ya mutu. Waɗanda suke masu shekara ɗari da haihuwa su ne samari. Waɗanda suka mutu kafin wannan lokaci, to, alama ce, ta cewa na hukunta su.

21-22. Mutane za su gina gidaje su kuwa zauna a cikinsu, ba waɗansu dabam za su mori gidajen ba. Za su dasa gonakin inabi su kuwa ji daɗin ruwan inabi, ba waɗansu dabam za su sha shi ba. Mutanena za su yi tsawon rai kamar itatuwa. Za su ci cikakkiyar moriyar abubuwan da suka yi aikinsu.

23. Aikin da suka yi zai yi nasara, 'ya'yansu ba za su gamu da bala'i ba, zan sa musu albarka duk da zuriyarsu har dukan zamanai.

Karanta cikakken babi Ish 65