Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 51:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji ya ce,“Ku kasa kunne gare ni, ku da kuke so a cece ku,Ku da kuka zo gare ni neman taimako.Ku yi tunanin dutse inda kuka fito,Da mahaƙar duwatsu inda kuka fito.

2. Ku yi tunani a kan kakanku Ibrahim,Da Saratu, wadda kuke zuriyarta.Sa'ad da na kira Ibrahim ba shi da ɗa,Amma na sa masa albarka, na ba shi 'ya'ya,Na sa zuriyarsa suka yi yawa.

3. “Zan ji juyayi a kan Sihiyona,Da dukan masu zama a kufanta.Ko da yake ƙasarta hamada ce, zan sa ta zama lambu,Kamar lambun da na dasa a Aidan.Murna da farin ciki za su kasance a can,Da waƙoƙi na yabo da godiya zuwa gare ni.

4. “Ku kasa kunne gare ni, ku mutanena,Ku saurara ga abin da nake faɗa,Na ba da koyarwata ga al'ummai,Dokokina za su kawo musu haske.

5. Zan zo da sauri in cece su,Lokacina na nasara ya yi kusa.Ni kaina zan yi mulki a kan al'ummai.Manisantan ƙasashe za su jira ni in zo,Za su jira da sa zuciya, ni in cece su.

6. Ku duba sammai, ku duba duniya!Sammai za su shuɗe kamar hayaƙi,Duniya kuwa za ta yage kamar tsohuwar tufa,Dukan mutanenta kuma za su mutu.Amma ceton da zan kawo zai dawwama har abada,Nasarata, ita ce za ta zama ta har abada.

7. “Ku kasa kunne gare ni, ku da kuka san abin da yake daidai,Ku da kuke riƙe da koyarwata a zuciyarku.Kada ku ji tsoro sa'ad da mutane suke yi muku ba'a da zagi.

8. Irin waɗannan mutane za su shuɗe kamar tufar da asu ya cinye!Amma ceton da zan kawo zai dawwama har abada,Nasarata za ta kasance har abada abadin.”

9. Ya Ubangiji, ka tashi, ka taimake mu!Ka nuna ikonka, ka cece mu,Ka nuna ikonka kamar yadda ka yi a dā.Kai ne ka daddatse dodon ruwa, wato Rahab.

10. Kai ne ka sa teku ta ƙafe,Ka kuma shirya hanya ta ruwa,Domin waɗanda kake cetonsu su haye.

11. Su waɗanda ka fansaZa su kai Urushalima da farin ciki,Da waƙa, da sowa ta murna.Za su yi ta murna har abada,Ba sauran baƙin ciki ko ɓacin zuciya har abada.

Karanta cikakken babi Ish 51