Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 41:10-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Kada ka ji tsoro, ina tare da kai,Ni ne Allahnka, kada ka bar kome ya firgita ka.Zan sa ka yi ƙarfi, in kuma taimake ka,Zan kiyaye ka, in cece ka.

11. “Su waɗanda suke fushi da ku, ku jama'ata,Za a ƙasƙantar da su su ji kunya.Waɗanda suke faɗa da ku kuwa za su mutu.

12. Za ku neme su, amma ba za ku same su ba,Wato waɗanda suke gāba da ku.Waɗanda suka kama yaƙi da ku,Za su shuɗe daga duniya.

13. Ni ne Ubangiji Allahnku,Na ƙarfafa ku, na kuwa faɗa muku,‘Kada ku ji tsoro, ni zan taimake ku.’ ”

14. Ubangiji ya ce,“Isra'ila, ku kima ne marasa ƙarfi kuma,Kada ku ji tsoro, zan taimake ku.Ni Allah Mai Tsarki na Isra'ila, ni ne mai fansarku.

15. Zan sa ku zama kamar abin sussuka,Wanda yake sabo, mai kaushi, mai tsini.Za ku sussuke duwatsu ku lalatar da su,Za a marmashe tuddai kamar ƙura.

16. Za ku watsa su sama cikin iska,Iska za ta hure su, ta tafi da su,Hadiri kuma zai warwatsar da su.Amma za ku yi murna, gama ni ne Allahnku,Za ku yabe ni, Allah Mai Tsarki na Isra'ila.

17. “Sa'ad da jama'ata ta bukaci ruwa,Sa'ad da maƙogwaronsu ya bushe da ƙishi,Sa'an nan ni Ubangiji, zan amsa addu'arsu,Ni Allah na Isra'ila, ba zan taɓa yashe su ba.

18. Zan sa kogunan ruwa su yi gudu daga ƙeƙasassun tuddai,Maɓuɓɓugan ruwa su yi gudu a kwaruruka.Zan sa hamada ta zama kududdufan ruwa,Busasshiyar ƙasa kuma ta zama maɓuɓɓugan ruwa.

19. Zan sa itatuwan al'ul su tsiro a hamada,Da itacen ƙirya, da itacen ci-zaki, da zaitun.Ƙeƙasasshiyar ƙasa za ta zama kurmi,Jejin itatuwan fir.

20. Mutane za su ga wannan, su sani,Ni Ubangiji, na yi shi.Za su fahimta,Allah Mai Tsarki na Isra'ila ya sa abin ya faru.”

21. Ubangiji, Sarki na Isra'ila, ya faɗi wannan,“Ku allolin al'ummai ku gabatar da matsalarku.Ku kawo dukan gardandamin da kuke da su!

22. Ku zo nan ku faɗi abin da zai faru nan gaba,Ku bayyana wa ɗakin shari'a abubuwan da suka riga sun faru,Ku faɗa mana yadda zai zama duka,Domin lokacin da ya faru mu mu sani.

23. Ku faɗa mana abin da gaba ta ƙunsa.Sa'an nan za mu sani, ku alloli ne!Ku aikata wani abu mai kyau, ko ku kawo wani bala'i,Ku cika mu da jin tsoro da fargaba!

24. Ku da dukan abin da kuke yi ba kome ba ne,Waɗanda suke yi muku sujada kuwa,Abin ƙyama ne su!

25. “Na zaɓi mutum wanda yake zaune a gabas,Zan kawo shi don ya kawo hari daga arewa.Zai tattake masu mulki su zama kamar lāka,Kamar yadda magini yake tattake yumɓu.

Karanta cikakken babi Ish 41