Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 37:26-38 Littafi Mai Tsarki (HAU)

26. “Ba ka taɓa sani, na riga na shirya a yi haka tuntuni ba? Yanzu ne kuwa na cika wannan. Ni na ba ka iko ka ragargaza birane masu kagarai su zama tsibin ɓuraguzai.

27. Mutanen da suke zaune a can marasa ƙarfi ne. Sun firgita, sun suma. Sun zama kamar ciyawa a saura, ko hakukuwan da suka tsiro a kan rufi, waɗanda zafin iskar gabas ta buga su.

28. “Amma na san kome game da kai, abin da kake yi da inda kake tafiya. Na san yadda ka harzuƙa gāba da ni.

29. Na sami labarin irin harzuƙarka da girmankanka, yanzu kuwa zan sa ƙugiya a hancinka, linzami kuma a bakinka, in komar da kai.”

30. Sa'an nan Ishaya ya ce wa sarki Hezekiya, “Ga alama a kan abin da zai faru. Da bana da baɗi sai gyauro za ku ci, amma a shekara ta biye za ku iya shuka hatsi ku kuma girbe shi, ku dasa kurangar inabi ku ci 'ya'yan.

31. Su da suka tsira daga al'ummar Yahuza za su yi lafiya kamar dashe-dashen da saiwoyinsu suka shiga da zurfi cikin ƙasa, suka kuma ba da amfani.

32. Mutanen da za su tsira su ne na cikin Urushalima da na kan Dutsen Sihiyona, gama Ubangiji Mai Runduna ne ya yi niyya ya sa haka ya faru.

33. “Wannan shi ne abin da Ubangiji ya ce a kan Sarkin Assuriya, ‘Ba zai shiga wannan birni ba, ko kuwa ya harba ko da kibiya ɗaya a cikinsa. Sojoji masu garkuwoyi ba za su zo ko kusa da birnin ba, ba kuma za su yi mahaurai kewaye da birnin ba.

34. Zai koma ta kan hanyar da ya zo, ba kuwa zai taɓa shiga wannan birni ba. Ni, Ubangiji, ni na faɗa.

35. Zan kāre wannan birni in kiyaye shi, saboda girmana, domin kuma alkawarin da na yi wa bawana Dawuda.’ ”

36. Mala'ikan Ubangiji kuwa ya shiga sansanin Assuriyawa ya kashe sojoji dubu ɗari da dubu tamanin da dubu biyar (185,000). Da asuba ta yi, sai ga su can kwankwance, duk sun mutu!

37. Sa'an nan sai Sarkin Assuriya, wato Sennakerib, ya janye ya koma Nineba.

38. Wata rana ya je yana sujada a gidan gunkinsa Nisrok, sai biyu daga cikin 'ya'yansa, Adrammelek da Sharezer, suka kashe shi da takubansu, sa'an nan suka tsere zuwa ƙasar Ararat. Wani daga cikin sauran 'ya'yansa, wato Esar-haddon, ya gāje shi ya zama sarki.

Karanta cikakken babi Ish 37