Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 37:20-30 Littafi Mai Tsarki (HAU)

20. Yanzu dai, ya Ubangiji Allahnmu, ka cece mu daga Assuriyawa domin dukan al'umman duniya su sani kai ne Allah kai kaɗai.”

21. Sa'an nan Ishaya ya aiki manzo zuwa wurin sarki Hezekiya, ya faɗa masa amsar Ubangiji a kan addu'ar sarki.

22. Ubangiji ya ce, “Birnin Urushalima yana yi maka dariya, kai Sennakerib, yana kuma yi maka ba'a.

23. Wa kake tsammani kana raina, kana yi masa ba'a? Ba ka ba ni girma ba, ni Allah mai tsarki na Isra'ila.

24. Ka aike da barorinka don su yi mini fāriya, da cewa ka ci nasara da duwatsu mafi tsayi da karusanka, har da ƙwanƙolin Dutsen Lebanon. Kana fāriya da cewa a can ka sare dogayen itatuwan al'ul da na fir, ka kuma kai wuri mafi nisa na jeji.

25. Ka kuma yi fāriya da cewa ka haƙa rijiyoyi a baƙuwar ƙasa, ka kuma sha ruwansu, sojojinka kuma sun tattake Kogin Nilu da ƙafafunsu, har ya ƙafe.

26. “Ba ka taɓa sani, na riga na shirya a yi haka tuntuni ba? Yanzu ne kuwa na cika wannan. Ni na ba ka iko ka ragargaza birane masu kagarai su zama tsibin ɓuraguzai.

27. Mutanen da suke zaune a can marasa ƙarfi ne. Sun firgita, sun suma. Sun zama kamar ciyawa a saura, ko hakukuwan da suka tsiro a kan rufi, waɗanda zafin iskar gabas ta buga su.

28. “Amma na san kome game da kai, abin da kake yi da inda kake tafiya. Na san yadda ka harzuƙa gāba da ni.

29. Na sami labarin irin harzuƙarka da girmankanka, yanzu kuwa zan sa ƙugiya a hancinka, linzami kuma a bakinka, in komar da kai.”

30. Sa'an nan Ishaya ya ce wa sarki Hezekiya, “Ga alama a kan abin da zai faru. Da bana da baɗi sai gyauro za ku ci, amma a shekara ta biye za ku iya shuka hatsi ku kuma girbe shi, ku dasa kurangar inabi ku ci 'ya'yan.

Karanta cikakken babi Ish 37