Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 35:5-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Makaho zai iya ganin gari,Kurma kuma zai iya ji.

6. Gurgu zai yi tsalle ya yi rawa,Waɗanda ba su iya magana za su yi sowa don murna.Rafuffukan ruwa za su yi gudu a cikin hamada,

7. Yashi mai ƙuna kuma zai zama tafki,Ƙeƙasasshiyar ƙasa kuma za ta cika da maɓuɓɓugai.Inda diloli suka yi zama,Ciyawar fadama da iwa za su tsiro.

8. Za a yi babbar karauka a can,Za a kira ta, “Hanyar Tsarki.”Ba mai zunubi da zai taɓa bi ta wannan hanya,Ba wawayen da za su ruɗar da waɗanda suke tafiya can.

9. Ba za a sami zakoki a can ba,Mugayen namomin jeji ba za su bi ta can ba.Waɗancan da Ubangiji ya fansarSu za su zo gida ta wannan hanya.

10. Za su kai Urushalima da murna,Suna raira waƙa suna sowa don murna.Za su yi farin ciki har abada,Ba damuwa da ɓacin rai har abada.

Karanta cikakken babi Ish 35