Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 22:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Wannan shi ne jawabi a kan kwarin wahayi.Me yake faruwa? Me ya sa jama'ar birni duka suke biki a kan rufin gidaje?

2. Birnin duka ya ruguntsume, cike da hayaniya da tashin hankali.Mutanenku da suka mutu ba su mutu suna yaƙi ba.

3. Dukan shugabanninku sun gudu, an kuwa kama su tun kafin su harba ko kibiya ɗaya. Dukanku da aka iske tare, aka kama ku, ko da yake kuka gudu da nisa.

4. Ni dai ƙyale ni kurum, in yi ta kuka mai zafi. Kada ka yi ƙoƙarin ta'azantar da ni, saboda yawancin mutanena sun mutu.

5. Wannan shi ne lokacin gigicewa, da shan ɗibga, da ruɗewa a cikin kwarin wahayi, Ubangiji Allah Mai Runduna shi ya aukar mana da shi. An ragargaza garukan birninmu har ƙasa, ana jin amsar kuwwar koke-kokenmu na neman taimako a cikin tsaunuka.

6. Sojojin ƙasar Elam sun zo kan dawakai suna rataye da kwari da baka. Sojojin ƙasar Kir sun shirya garkuwoyinsu.

7. Kwarurukansu masu dausayi na ƙasar Yahuza suna cike da karusai, sojoji kuma a kan dawakai suna tsattsaye a ƙofofin Urushalima.

8. Dukan kagaran Yahuza sun rushe.Sa'ad da wannan ya faru kun kwaso makamai daga cikin taskar makamai.

9-10. Kun ga wuraren da suke bukatar gyara a garukan Urushalima. Ku ƙidaye dukan gidaje da suke cikin Urushalima, kuka rushe waɗansu gidaje don ku sami duwatsun da za ku gyara garukan Urushalima. Don ku tanada ruwa a cikin birnin,

11. kun gina matarar ruwa a jikin garuka don ta tare ruwan da yake gangarowa daga tsohon tafki. Amma ba ku kula da Allah ba, wanda ya shirya wannan tuntuni, wanda kuma ya sa wannan ya kasance.

Karanta cikakken babi Ish 22