Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 11:7-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Shanu da beyar za su yi kiwo tare,'Yan maruƙansu da kwiyakwiyansu za su kwanta lafiya.Zaki zai ci ciyawa kamar sā.

8. Jariri zai yi wasa kusa da maciji mai mugun dafiAmma ba zai cuta ba.

9. A kan Sihiyona, dutse tsattsarka,Ba wani macuci ko mugu.Ƙasar za ta cika da sanin UbangijiKamar yadda tekuna suke cike da ruwa.

10. Rana tana zuwa sa'ad da sabon sarki zai fito daga cikin gidan sarautar Dawuda, zai zama alama ga sauran al'umma. Za su tattaru a birnin sarautarsa su girmama shi.

11. A wannan rana Ubangiji zai sāke zuwa, ya nuna ikonsa. Zai komo da mutanensa gida waɗanda suka ragu a Assuriya, da Masar, da ƙasashen Fatros, da Habasha, da Elam, da Babila, da Hamat, da kuma ƙasashen bakin gāɓa da na tsibiran teku.

12. Ubangiji zai ɗaga tuta, alama ce ta nuna wa sauran al'umma, ya sāke tattara jama'ar Isra'ila da ta Yahuza waɗanda aka warwatsa, ya sāke komo da su daga kusurwoyi huɗu na duniya.

13. Masarautar Isra'ila ba za ta ƙara jin kishin Yahuza ba, Yahuza kuma ba za ta zama abokiyar gābar Isra'ila ba.

14. Tare za su fāɗa wa Filistiyawa da yaƙi daga yamma, su washe mutanen da suke wajen gabas. Za su ci nasara a kan mutanen Edom da na Mowab, jama'ar Ammon kuwa za su yi musu biyayya.

15. Ubangiji zai kawo iska mai zafi wadda za ta busar da Kogin Nilu, da na Yufiretis. Zai bar ƙananan rafuffuka bakwai ne kaɗai, don kowa da kowa ya taka ya haye.

16. Za a yi babbar karauka daga Assuriya domin sauran mutanen Isra'ila da suka ragu a can, kamar yadda aka yi wa kakanninsu sa'ad da suka bar Masar.

Karanta cikakken babi Ish 11