Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 49:14-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Irmiya ya ce,“Na karɓi saƙo daga wurinUbangiji.An aiki jakada a cikin al'ummaicewa,‘Ku tattara kanku, ku zo ku yi gābada ita,Ku tasar mata da yaƙi!’

15. Gama ga shi, zan maishe kiƙanƙanuwa cikin al'ummai,Abar raini a wurin mutane.

16. Tsoronki da ake ji da girmankankisun ruɗe ki,Ke da kike zaune a kogon dutse, akan tsauni,Ko da yake kin yi gidanki can samakamar gaggafa,Duk da haka zan komar da ke ƙasa,Ni Ubangiji na faɗa.”

17. Ubangiji ya ce, “Edom za ta lalace, duk wanda ya bi ta wurin zai gigice, ya yi tsaki saboda dukan masifunta.

18. Abin da zai faru ga Edom zai zama daidai da abin da ya faru ga Saduma, da Gwamrata, da biranen da suke kusa da su, a lokacin da aka kaɓantar da su. Ba wanda zai zauna cikinta, ba wanda kuma zai yi zaman baƙunci a cikinta, ni Ubangiji na faɗa.

19. Kamar yadda zaki yakan fito daga cikin kurmin Urdun, garin ya fāda wa babban garken tumaki, haka zan sa nan da nan su gudu daga gare ta. Zan naɗa wani wanda na zaɓa, gama wa yake kama da ni? Wa zai yi ƙarata? Ina makiyayin da ya isa ya yi gāba da ni?

20. Domin haka, ku ji shirin da ni Ubangiji na yi wa Edom, da abin da nake nufin yi wa mazaunan Teman. Hakika za a tafi da su, har da ƙanana na garken tumaki, zan kuma sa wurin kiwonsu ya zama ƙeƙuwa saboda su.

21. Amon fāɗuwarsu zai sa ƙasa ta girgiza, za a kuma ji muryar kukansu har a Bahar Maliya.

22. Wani zai tashi da sauri, ya yi sama kamar gaggafa. Zai buɗe fikafikansa a kan Bozara. Zukatan sojojin Edom za su zama kamar zuciyar macen da take naƙuda.”

23. Ga abin da Ubangiji ya faɗa a kan Dimashƙu,“Hamat da Arfad sun gigice,Domin sun ji mugun labari,sun narke saboda yawan damuwa,Ba za su iya natsuwa ba.

24. Dimashƙu ta yi halin ƙaƙa naka yi,Ta juya, ta gudu,Tsoro ya kama ta,Azaba da baƙin ciki sun kama takamar na naƙuda.

25. Ƙaƙa aka manta da sanannen birni,Birnin da take cike da murna?

26. A waccan rana samarinta za su fāɗi adandalinta.Za a hallaka sojojinta duka,Ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.

27. Zan kuma sa wuta a garun Dimashƙu,Za ta kuwa cinye fādodinBen-hadad.”

Karanta cikakken babi Irm 49