Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 41:7-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Sa'ad da suka shiga birnin, sai Isma'ila ɗan Nataniya da mutanen da suke tare da shi suka kashe su, suka jefa su a wata rijiya.

8. Amma waɗansu mutum goma daga cikinsu suka ce wa Isma'ila, “Kada ka kashe mu, gama muna da rumbunan alkama, da na sha'ir, da kuma man zaitun da zuma a ɓoye a cikin gonaki.” Sai ya bar su, bai kashe su tare da abokansu ba.

9. Rijiyar da Isma'ilu ya zuba dukan gawawwakin mutanen da ya kashe mai zurfi ce, sarki Asa ne ya haƙa saboda tsoron Ba'asha Sarkin Isra'ila. Isma'ilu ɗan Netaniya kuwa ya cika ta da gawawwakin mutanen da ya kashe.

10. Sai Isma'ilu ya kwashe dukan sauran mutanen da suke Mizfa, gimbiyoyi da dukan jama'ar da aka bari a Mizfa, waɗanda Nebuzaradan, shugaban matsara, ya bari a hannun Gedaliya ɗan Ahikam. Isma'ilu ɗan Netaniya ya kwashe su ganima, ya haye da su zuwa yankin Ammonawa.

11. Amma sa'ad da Yohenan ɗan Kareya, tare da dukan shugabannin sojoji da suke tare da shi suka ji irin wannan mugun aiki wanda Isma'ilu ɗan Netaniya ya yi,

12. sai suka kwashe mutanensu duka, suka tafi su yi yaƙi da Isma'ilu ɗan Netaniya. Suka iske shi a babban tafkin da take a Gibeyon.

13. Sa'ad da dukan jama'ar da Isma'ilu ya kwashe suka ga Yohenan ɗan Kareya, da dukan shugabannin sojoji tare da shi, sai suka yi murna.

14. Dukan mutanen nan da Isma'ilu ya kwashe su ganima daga Mizfa, suka juya, suka koma wurin Yohenan ɗan Kareya.

15. Amma Isma'ilu ɗan Netaniya tare da mutum takwas suka tsere suka gudu zuwa wurin Ammonawa.

16. Sai Yohenan ɗan Kareya da dukan shugabannin sojoji da suke tare da shi, suka kwashe dukan sauran jama'a, waɗanda Isma'ilu ɗan Netaniya ya kamo daga Mizfa bayan ya kashe Gedaliya ɗan Ahikam, wato sojoji da mata, da yara, da bābāni, su ne Yohenan ya komo da su daga Gibeyon.

17. Suka fa tafi suka zauna a wurin Kimham kusa da Baitalami. Suna nufin su tafi Masar,

Karanta cikakken babi Irm 41