Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 34:3-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Ba za ka tsere masa ba, amma lalle za a kama ka, a ba da kai a hannunsa. Za ka ga Sarkin Babila ido da ido, ka kuma yi magana da shi fuska da fuska. Za ka tafi Babila.

4. Ya Zadakiya, Sarkin Yahuza, ka ji maganar da ni Ubangiji na faɗa a kanka, ba za ka mutu ta wurin takobi ba.

5. Za ka mutu da salama. Kamar yadda aka ƙona wa sarakuna marigayanka turare, haka kai ma mutane za su ƙona maka turare, za su yi makoki dominka suna cewa, ‘Kaito, sarki ya rasu.’ Ni Ubangiji na faɗa.”

6. Sai annabi Irmiya ya faɗa wa Zadakiya, Sarkin Yahuza, dukan maganan nan a Urushalima,

7. sa'ad da sojojin Sarkin Babila suke yaƙi da Urushalima da kuma dukan biranen da suka ragu na Yahuza, wato Lakish da Azeka. Waɗannan su kaɗai ne biranen Yahuza masu garu da suka ragu.

8. Ubangiji kuma ya yi magana da Irmiya bayan da Zadakiya ya yi alkawari da dukan mutanen Urushalima don a yi musu shelar ba da 'yanci,

9. cewa kowa ya saki bayinsa, mata da maza, waɗanda suke Yahudawa. Kada kowa ya riƙe bawa wanda yake Bayahude, ɗan'uwansa.

10. Sai suka yi biyayya. Dukan sarakuna da dukan jama'a waɗanda suka yi alkawarin, cewa kowa zai 'yantar da bawansa ko baiwarsa, ba za su ƙara bautar da su ba, suka yi biyayya, suka 'yantar da su.

11. Daga baya kuwa suka sāke komo da waɗannan bayi, mata da maza waɗanda suka 'yantar, suka kuma mai da su bayi.

12. Ubangiji ya yi magana da Irmiya, ya ce,

13. “Ni Ubangiji Allah na Isra'ila, na yi alkawari da kakanninku lokacin da na fito da su daga ƙasar Masar daga bauta, na ce,

14. ‘A shekara ta bakwai, dole ne ku 'yantar da 'yan'uwanku, Ibraniyawa, waɗanda aka sayar muku, suka kuwa bauta muku shekara shida. Dole ne ku 'yantar da su daga bautarku.’ Amma kakanninku ba su kasa kunne gare ni ba.

15. A 'yan kwanakin da suka wuce kuka yi abu mai kyau a gabana da kuka tuba, har kuka yi wa juna shelar 'yanci. Kuka yi alkawari a gabana a Haikalin da ake kira da sunana.

16. Amma sai kuka sāke tunaninku, kuka ɓata sunana sa'ad da kowannenku ya komo da bayinsa, mata da maza, waɗanda kuka 'yantar, don su zauna yadda suke so. Ga shi kuma, kun komo da su su zama bayinku.

17. Domin haka ni Ubangiji na ce, ba biyayya kuka yi mini ba, da irin shelar 'yancin da kowannenku ya yi wa ɗan'uwansa da maƙwabcinsa, saboda haka ni zan yi muku shelar 'yanci zuwa mutuwa ta takobi, da annoba, da yunwa. Zan sa ku zama abin ƙyama ga dukan mulkokin duniya.

Karanta cikakken babi Irm 34