Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 25:5-30 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. yana cewa, ‘Sai kowane ɗayanku ya juyo daga mugun halinsa da mugayen ayyukansa don ya zauna a ƙasar da Ubangiji ya ba ku, ku da kakanninku tun daga zamanin dā har abada.

6. Kada ku bi gumaka, ku bauta musu, ku yi musu sujada, ko ku tsokane ni da ayyukan hannuwanku, sa'an nan ba zan hore ku ba.’

7. Duk da haka ba ku kasa kunne gare shi ba, shi Ubangiji ya faɗa, sai kuka tsokane shi da ayyukan hannuwanku. Wannan kuwa zai cuce ku.

8. “Domin haka Ubangiji Mai Runduna ya ce, ‘Tun da yake kun ƙi yin biyayya da maganata,

9. zan aiko kabilai daga arewa da bawana Nebukadnezzar, Sarkin Babila. Zan kawo su, su yi yaƙi da ƙasan nan da mazaunanta, da dukan al'umman da take kewaya da ita. Zan hallaka su sarai, in sa su zama abin ƙyama, da abin raini, da abin zargi har abada.

10. Banda haka zan kawar da muryar sowa da ta farin ciki, da ta ango da ta amarya, da amon dutsen niƙa daga gare su. Zan kashe hasken fitilunsu.

11. Ƙasar duka za ta zama kufai marar amfani, waɗannan al'ummai za su bauta wa Sarkin Babila har shekara saba'in.

12. Sa'an nan bayan cikar shekara saba'in ɗin, zan hukunta Sarkin Babila da ƙasarsa, wato ƙasar Kaldiyawa. Zan maishe ta kango har abada, saboda zunubinsa.

13. Zan kawo wa wannan ƙasa dukan abin da na faɗa gāba da ita. Dukan abin da aka rubuta a wannan littafi, wato dukan abin da Irmiya ya yi annabcinsa gāba da dukan al'umman nan.

14. Al'ummai da yawa da manyan sarakuna za su bautar da su, ni kuwa zan yi musu sakayya bisa ga ayyukan hannuwansu.’ ”

15. Ubangiji Allah na Isra'ila ya ce mini, “Ka karɓi ƙoƙon ruwan inabin nan na fushina a wurina, ka sa dukan al'umman da na aike ka gare su, su sha.

16. Za su sha, su yi tangaɗi su yi hauka saboda takobin da zan aiko a cikinsu.”

17. Sai na karɓi ƙoƙon daga wurin Ubangiji, na sa dukan al'umman da Ubangiji ya aike ni gare su, su sha daga cikinsa.

18. Urushalima, da biranen Yahuza, da sarakunanta, da shugabanninta, za su zama kango da abin ƙyama da abin raini, da abin la'ana. Haka yake a yau.

19-26. Ga lissafin sauran da za su shaƙoƙon.Fir'auna Sarkin Masar da kumabarorinsa, da sarakunansa,Dukan jama'arsa, da dukanbaƙin da suke tare da su,dukan sarakunan ƙasar Uz,dukan sarakunan ƙasarFilistiyawa, wato Ashkelon, daGaza, da Ekron, da saura naAshdod,Edom da Mowab, da 'ya'yanAmmon maza,dukan sarakunan Taya, da dukansarakunan Sidon,dukan sarakunan da suke gaɓarBahar Rum da waɗanda suke atsibiran tekun,Dedan, da Tema, da Buz, dadukan waɗanda suke yi wakansu sanƙo,dukan sarakunan Arabiya,dukan sarakunan tattarmukanmutane da suke zaune ahamada,dukan sarakunan Zimri, da dukansarakunan Elam, da dukansarakunan Mediya,dukan sarakunan arewa, na nesada na kusa bi da bi.Dukan mulkokin da suke fuskar duniya za su sha daga ciki. Daga nan sai Sarkin Babila a bayansu duka, zai sha nasa.

27. “Za ka kuma faɗa musu cewa, ‘In ji Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ku sha, ku bugu, ku yi amai, ku fāɗi, kada kuma ku tashi saboda takobin da zan aiko muku.’

28. Idan kuwa sun ƙi su karɓi ƙoƙon daga hannunka su sha sai ka faɗa musu cewa, ‘Ubangiji Mai Runduna ya ce, dole ne ku sha!

29. Gama ga shi, na fara sa masifa ta yi aiki cikin birnin da ake kira da sunana. To, kuna tsammani ba za a hukunta ku ba? Sai an hukunta ku, gama ina kawo wa dukan mazaunan duniya takobi. Ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.’

30. “Kai Irmiya kuma sai ka yi annabcin dukan waɗannan magana gāba da su, ka faɗa musu cewa,‘Ubangiji zai yi ruri daga Sama,Zai yi magana daga wurin zamansamai tsarki,Zai yi wa garkensa ruri da ƙarfiƙwarai,Zai yi ihu kamar masu matse'ya'yan inabi,Zai yi gāba da dukan mazaunanduniya.

Karanta cikakken babi Irm 25