Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 13:7-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Sai na tafi Yufiretis, na haƙa na ɗauko abin ɗamara daga wurin da na ɓoye shi. Amma abin ɗamara ya lalace, ba shi da sauran amfani.

8. Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce,

9. “Haka zan lalatar da alfarmar Yahuza da yawan alfarmar Urushalima.

10. Wannan muguwar jama'a, wadda ta ƙi jin maganata, wadda ta taurare, ta bi son zuciyarta, ta kuma bi gumaka ta bauta musu, ta yi musu sujada, za ta zama kamar abin ɗamaran nan, wanda ba shi da sauran amfani.

11. Gama kamar yadda abin ɗamara yakan kame tam a gindin mutum, haka na sa dukan mutanen Isra'ila da dukan mutanen Yahuza su manne mini domin su zama jama'a, da suna, da yabo, da daraja a gare ni, amma sun ƙi ji.”

12. “Sai ka faɗa musu wannan magana cewa, ‘Ni Ubangiji Allah na Isra'ila na ce, a cika kowane tulu da ruwan inabi.’ Su kuwa za su ce maka, sun sani sarai za a cika kowane tulu da ruwan inabi.

13. Sa'an nan za ka faɗa musu, Ubangiji ya ce, ‘Ga shi, zan sa dukan mazaunan ƙasar su bugu da ruwan inabi, wato sarakunan da suka hau gadon sarautar Dawuda, da firistoci, da annabawa, da dukan mazaunan Urushalima.

Karanta cikakken babi Irm 13