Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 9:18-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. Gobe war haka zan sa a yi ƙanƙara mai tsananin gaske irin wadda Masar ba ta taɓa gani ba tun kafawarta, har zuwa yanzu.

19. Yanzu fa, sai ka ba da umarni a lura da awaki, da dukan abin da yake naku wanda yake a saura, gama duk mutum ko dabba wanda ya ragu a saura, wato wanda ba a kawo shi gida ba, zai mutu sa'ad da ƙanƙarar ta zo.”’

20. Akwai waɗansu daga cikin fādawan Fir'auna waɗanda suka tsorata saboda abin da Ubangiji ya faɗa, sai suka kawo bayinsu da dabbobinsu cikin gida.

21. Amma waɗanda ba su kula da abin da Ubangiji ya faɗa ba, suka bar bayinsu da dabbobinsu a waje cikin saura.

22. Sa'an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Miƙa hannunka sama don a yi ƙanƙara a bisa mutum da dabba da bisa dukan itatuwan saura a dukan ƙasar Masar.”

23. Sai Musa ya miƙa sandansa sama, Ubangiji kuwa ya aiko da tsawa da ƙanƙara, wuta kuwa ta bi ƙasar. Ubangiji ya sa aka yi ƙanƙara a bisa ƙasar Masar.

24. Ƙanƙarar tana faɗowa, wuta kuma tana tartsatsi a cikin ƙanƙara. Aka yi ƙanƙara mai tsananin gaske irin wadda ba a taɓa yi ba cikin dukan ƙasar Masar tun lokacin da ta zama al'umma.

25. Ƙanƙarar ta bugi ko'ina a Masar. Dukan abin da yake cikin saura, mutum duk da dabba, da tsire-tsire duka, ƙanƙara ta buge su. Duk itatuwan da yake a saura aka ragargaza su.

26. Sai dai a ƙasar Goshen inda Isra'ilawa suke, ba a yi ƙanƙara ba.

27. Fir'auna ya aika, aka kirawo Musa da Haruna, ya ce musu, “Lalle a wannan karo na yi laifi, Ubangiji shi ne da gaskiya. Ni da jama'ata muke da kuskure.

28. Ku roƙi Ubangiji ya tsai da tsawar da ƙanƙarar. Ni kuwa na yi alkawari zan bar ku ku tafi, ba za ku ƙara tsayawa a nan ba.”

29. Musa ya ce masa, “Da fitata daga cikin birnin, zan yi addu'a ga Ubangiji, walƙiya kuwa za ta tsaya, ƙanƙara kuma ta daina, don ku sani duniya ta Ubangiji ce.

30. Amma dai na sani, da kai da fādawanka, har wa yau ba ku ji tsoron Ubangiji Allah ba tukuna.”

31. Rama da sha'ir suka lalace, gama sha'ir ya riga ya nuna, rama kuwa tana huda.

Karanta cikakken babi Fit 9