Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 8:24-32 Littafi Mai Tsarki (HAU)

24. Haka kuwa Ubangiji ya aikata. Ƙudaje masu yawa suka shiga gidan Fir'auna, da gidan fādawansa, da ko'ina a ƙasar Masar. Ƙasar kuwa ta lalace saboda ƙudaje.

25. Sa'an nan Fir'auna ya kirawo Musa da Haruna, ya ce, “Tafi, ku yi wa Allahnku hadaya a ƙasan nan.”

26. Amma Musa ya ce, “Ba zai kyautu a yi haka ba, gama irin dabbobin da za mu miƙa wa Ubangiji Allahnmu hadaya da su, haramu ne ga Masarawa. Idan fa muka miƙa hadaya da waɗannan dabbobi da suke haramu a idon Masarawa za su jajjefe mu da duwatsu.

27. Za mu yi tafiya kwana uku a jeji kafin mu miƙa hadaya ga Ubangiji Allahnmu kamar yadda ya umarce mu.”

28. Sai Firauna ya ce, “Zan bar ku ku tafi, ku miƙa wa Ubangiji Allahnku hadaya a jeji, sai dai kada ku tafi da nisa. Ku kuma yi mini addu'a.”

29. Musa kuwa ya ce, “Nan da nan da tashina daga gabanka, zan yi addu'a ga Ubangiji, ƙudajen kuwa za su rabu da kai, da fādawanka, da jama'arka gobe, kada ka sāke yin ruɗi, ka ƙi barin jama'ar su tafi, su miƙa wa Ubangiji hadaya.”

30. Musa ya fita daga wurin Fir'auna, ya roƙi Ubangiji.

31. Ubangiji kuwa ya aikata bisa ga roƙon Musa. Ƙudajen suka rabu da Fir'auna, da fādawansa, da jama'arsa. Ko ƙuda ɗaya bai ragu ba.

32. Duk da haka Fir'auna ya taurare zuciyarsa a wannan lokaci kuma, ya ƙi sakin jama'ar.

Karanta cikakken babi Fit 8